Manyan 'Yan Siyasa a Najeriya da Kungiyoyin Kwallon da Suke Goyon Baya a Gasar Firimiya
FCT, Abuja - Gasar firimiyan Ingila (EPL) ta zama daya daga cikin wasannin kwallon kafa da aka fi kallo a duniya a zamanin nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Najeriya ba a bar ta a baya ba, inda take ɗaya daga cikin ƙasashen da ake kallon gasar a duniya.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta lissafo shahararrun ƴan siyasan Najeriya guda shida da ƙungiyoyin kwallon Ingilar da suke goyon baya.
1. Festus Keyamo (Arsenal)
Festus Keyamo babban lauya ne (SAN) kuma yana riƙe da muƙamin ministan sufurin jiragen sama tun shekarar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Afrilu na 2018, an naɗa shi a matsayin daraktan hulɗa da jama’a na yaƙin neman zaɓen tazarcen tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a 2019, daga baya kuma aka naɗa shi ministan ƙwadago da ayyukan yi.
Festus Keyamo yana goyon bayan ƙungiyar Arsenal ta ƙasar Ingila wanda ta ke ta biyu a teburi.
2. Atiku Abubakar (Arsenal)
Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.
Ya yi takarar gwamnan jihar Adamawa a 1990 da 1996 amma bai yi nasara ba, sai a shekarar 1999 ya samu nasara.
Kafin a rantsar da shi, aka dauko shi a matsayin mataimakin Olusegun Obasanjo a zaɓen 1999, kuma an sake zaɓensa a 2003.
Atiku ya yi takarar shugaban ƙasa sau shida (1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023) amma bai taɓa samun nasara ba.
Jigon na jam’iyyar PDP, yana goyon bayan ƙungiyar Arsenal, kuma yana yawan nuna farin cikinsa a shafukan sada zumunta a duk lokacin da Arsenal ta yi bajinta.
3. Bukola Saraki (Arsenal)
Bukola Saraki wanda ya kasance shugaban majalisar dattawan Najeriya daga 2015 zuwa 2019, yana goyon bayan ƙungiyar Arsenal.
Bukola Saraki ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan jihar Kwara daga shekarar 2003 zuwa 2011.
Bukola Saraki yana da ƙungiyarsa ta kwallon kafa a Najeriya mai suna Abubakar Bukola Saraki (ABS) Ilorin Football Club.
4. Babatunde Raji Fashola (Manchester United)
Babatunde Raji Fashola (SAN) wanda ya taɓa riƙe ministan ayyuka da gidaje daga 2019 zuwa 2023 yana goyon bayan ƙungiyar Manchester United.
Ya kuma riƙe muƙamin gwamnan jihar Legas na tsawon wa’adin shekaru takwas (2007 - 2015).
Fashola babban magoyin bayan Manchester United ne, kuma ya taɓa gayyatar gayyaci tsohon ɗan kwallon Ingila, Rio Ferdinand, zuwa Legas.
5. Dino Melaye (Arsenal)
Dino Melaye tsohon sanata ne, wanda ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2015.
Melaye wanda ɗan asalin Ayetoro Gbede ne daga ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi, yana goyon bayan ƙungiyar Arsenal.
A shekarar 2015, ya sauya sheƙa zuwa APC, amma ya koma jam'iyyar PDP kafin zaɓen 2019 sakamakon rikicin da yake da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
A shekarar 2023, ya yi takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, inda ya zo na uku.
6. Babajide Sanwo-Olu (Arsenal)
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, yana goyon bayan ƙungiyar Arsenal a gasar firimiyan Ingila.
Babajide Sanwo-Olu ya zama gwamnan jihar Legas a shekarar 2019, sannan ya sake yin tazarce bayan lashe zaɓe a farkon 2023.
Kwanan nan aka gan shi yana tsokanan Didier Drogba wanda ya addabi Arsenal a lokacin da yake bugawa kungiyar Chelsea wasa.
7. Terver Akase (Manchester United)
Terver Akase hadimi ne ga tsohon gwamnan hihar Benue, Samuel Ortom.
Akase mamba ne na jam’iyyar PDP, kuma yana daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamnan jihar Benue a zaɓen 2023.
Yana yawan wallafa ra’ayinsa a shafukan sada zumunta kan ƙungiyarsa ta Manchester United.
Ƴan Afirika da suka yi suna a gasar firimiya
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo muku jerin ƴan ƙasashen Afirika da suka yi suna a gasar firimiyan Ingila.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT
Gasar firimiyar Ingila dai, masana harkar ƙwallon ƙafa sun tabbatar da cewa ita ce wacce ta fi ɗaukar hankali a nahiyar Turai.
Ƴan Afirika da dama sun taka leda a gasar firimiya, inda da yawa daga cikinsu suka yi fice bayan sun kwace shekaru suna buga wasa a gasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng