
Dino Melaye







A zaben Nuwamban 2023 da za a shirya, Sanata Dino Melaye ya samu takarar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin Jam’iyyar PDP. Dino Melaya zai tunkari Ahmad Usman-Ododo

Dan takarar gwamnan Kogi, Dino Melaye ya bayyana yadda Gwamna Nyesom Wike ya roke shi don ya tabbata Atiku Abubakar ya dauke shi a matsayin abokin takararsa.

Sanata Dino Melaye, daya daga cikin neman tikitin PDP a zaben gwamnan Kogi ya caccaki Gwamna Nyesom Wike saboda furucin da ya yi a kansa a baya-bayan nan.

Gwamna Nyesom Wike ya yi watsi da yiwuwar nasarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kogi idan har ta ba Dino Melaye tikitinta.

Dan takarar shugaban kasa na PDP ya bayyana cewa, a halin da ake ciki bashi da wani dan takarar gwamnan da yake goyon baya a zaben na gwamnan Kogi da ke tafe.

Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci gwamnonin PDP, G5 da su janye daga yi masa ba’a don ya fadi zaben shugaban kasa cewa ai su ma sun sha kaye a zabensu na sanata.

Dino Melaye ya ce canjin kudi da aka fito da shi gabanin zabe ba yaudara ne. Mai magana da yawun Atiku-Okowa a jam’iyyar PDP ya ce sun kashe N400bn a kamfe.

Dino Melaye, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben takarar shugaban kasa na Atiku-Okowa ya ba wa marada kunya ya kawo wa maigidansa ,Atiku, akwatinsa.

Sanata Dino Melaye ya wallafa bidiyon katafaren gidansa da ke kauyensa a jihar Kogi a Facebook. Akwai ainahin gini, masaukin baki mai dakuna shida da sauransu.
Dino Melaye
Samu kari