Cikakken Sunayen ’Yan Kwallon Nahiyar Afirka 8 da Su Ka Fi Shura a Gasar Firimiya Ta Ingila

Cikakken Sunayen ’Yan Kwallon Nahiyar Afirka 8 da Su Ka Fi Shura a Gasar Firimiya Ta Ingila

Landan, Ingila - Gasar Firimiya ta kasar Ingila na daga cikin gasa mafi buguwa a duniyar kwallon kafa wanda mafi yawan 'yan kwallon ke son taka leda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Masana sun tabbatar da cewa a yanzu haka babu gasar da tafi daukar hankali a Nahiyar Turai kamar ta Firimiya.

Jerin hazikan 'yan kwallon Afirka da su ka yi shura a gasar Firimiya
Yan Kwallon Nahiyar Afirka da Su Ka Yi Shura a Gasar Firimiya. Hoto: Liverpool FC, Chelsea FC.
Asali: Facebook

Hakan ya faru ne saboda yadda ko wace kungiar kwallon kafa a gasar ke yunwar yin nasara da kuma neman daga kofin gasar, cewar The Nation.

Legit Hausa ta tattaro muku jerin 'yan kwallon Afirka da su ka yi shura a gasar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Mohammed Salah

Babu abin mamaki dan Salah ya kasance na farko bayan ya zura kwallaye 137 a wasanni 218 ga kungiyar Liverpool a gasar, cewar BBC.

Kara karanta wannan

‘Yan Kasuwa Sun Koka Game da Asarar N13bn da Ake Yi a Mako Saboda Rufe Iyakoki

Salah ya samu kyautar wanda ya fi kowa shan kwallaye har sau uku, a shekarar 2018 ya samu kyautar wanda ya fi kowa cin kwallo mai kyau inda aka ba shi kyautar 'Puskas'.

Dan kwallon Masar din shi ya fara cin kyautar a kungiyar Liverpool, sannan ya zama ɗan wasa na farko da ya sha kwallaye 32 a wasanni 38.

2. Didier Drogba

Drogba ya kware wurin shan kwallaye ta sama wanda ya kasance dan wasan gaba da aka fi tsoro a lokacinsa na tsawon shekaru.

Dan kasar ta Ivory Coast ya sha kwallaye 164 a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

3. Yaya Toure

Toure wanda shi ma dan kasar Ivory Coast ne ya fara shura a kungiyar Barcelona inda ya ci gasar Laliga biyu da gasar Zakarun Turai a 2007.

Dan wasan tsakiyar ya dawo kungiyar Manchester City inda ya buga wasanni 230.

4. Kolo Toure

Kara karanta wannan

Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli, Hukumar NJC ta yi abu 1 don inganta bangaren shari'a

Dan uwa ga Yaya ya shafe shekaru 14 a gasar ta Firimiya a matsayin dan wasan baya, cewar The Capital.

Kolo ya ci gasar Firimiya har sau biyu a kungiyoyin Arsenal da Manchester City wanda ake ganin na daga cikin hazikan 'yan wasan baya a gasar.

5. Sadio Mane

Kafin barin gasar Firimiya, Mane ya lashe kofunan Firimiya da gasar Zakarun Turai da FA da gasar UEFA duk a kungiyar Liverpool.

A yanzu ya na kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr bayan ya bar kungiyar Bayern Munich a kakar bara.

6. Riyard Mahrez

Mahrez na daga cikin zaratan 'yan wasan da su ka ci gasar Firimiya da kungiyar Leicester City a shekarar 2016.

Dan wasan Algeriya ya na buga tambola a yanzu a kungiyar Manchester City wanda a yanzu su ke kan ganiyarsu.

7. Michael Essien

Essien na daga cikin zaratan 'yan kwallo da su ka yi tashe lokacin da Chelsea ke kan kaifinta a duniyar kwallon kafa.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Dattawan Arewa sun fadi abin da ya kamata manyan sojoji su yi, sun fadi dalilansu

Essien wanda dan kasar Ghana ne ya kware a fannin rike kwallo a tsakiyar fili a matsayin dan wasan tsakiya.

8. Pierre-Emerick Aubameyang

Aubameyang ya yi bajinta a lokacin da ya ke kungiyar Arsenal bayan ya sha kwallaye 68 a wasanni 128.

Shekarar da dan wasan na Gabon ya fi shura ita ce 2018 zuwa 2019 inda ya sha kwallaye 22 da hakan ya ba shi damar shiga jerin mafi shan kwallaye a Afrika a shekarar.

Dan kwallon kafa ya mutu ya na atisaye

A wani labarin, wani dan wasan kwallon kafa ya mutu yayin da ya ke tsaka da atisaye a jihar Ogun.

Marigayin mai suna Sodiq Adebisi ya rasu ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel