Magana Ta Zo Karshe: Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan N77,000

Magana Ta Zo Karshe: Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan N77,000

  • Shugaban hukumar kula masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ya yi albishir ga matasan da ke hidimtawa ƙasar nan na shekara ɗaya
  • Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya tabbatar da cewa za a fara biyan matasa ƴan NYSC alawus na N77,000 duk wata daga watan Fabrairun 2025
  • Shugaban na NYSC ya ba da tabbacin cewa an sanya ƙarin a cikin kasafin kudin shekarar 2025, kuma za a fara aiwata da shi daga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya yi magana kan lokacin fara biyan N77,000.

Shugaban na hukumar NYSC ya tabbatarwa matasan da ke yi wa ƙasa hidima cewa za su fara karɓar N77,000 daga watan Fabrairun 2025.

Za a biya 'yan NYSC sabon alawus
Shugaban NYSC ya ce za a fara biyan N77,000 daga Fabrairu Hoto: @officialnyscng
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya bayyana hakan ne a sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Jinkiri ya kare: Gwamnati ta fadi watan da matasa ƴan NYSC za su fara karbar N77000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta yi jinkirin biyan sabon alawus

Biyo bayan amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin alawus na masu yin NYSC daga N33,000 zuwa N77,000.

Sai dai, mutane da dama sun nuna damuwa kan rashin aiwatar da wannan ƙarin da gwamnatin tarayya ta yi.

A shekarar da ta gabata, wani jami’in NYSC ya danganta jinkirin fara biyan sabon alawus ɗin kan rashin isassun kuɗi.

Za a biya ƴan NYSC N77,000

Amma yayin da yake jawabi ga matasa masu yi wa ƙasa hidima na rukunin B, 'Stream II', a jihar Katsina, shugaban na NYSC ya tabbatar da cewa an sanya ƙarin alawus ɗin a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.

Ya bayyana cewa za a fara biyan sabon alawus ɗin da zarar an amince da kasafin kuɗin 2025, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Gwamnatin Tarayya ta riga ta amince da ƙarin alawus ɗinku. Wannan ba sabuwar magana ba ce, muna da amincewar a hannu. Abin da muke jira kawai shi ne amincewa da kasafin kuɗi."

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

"Wannan watan (Janairu) ya riga ya kare, amma da zarar an amince da kasafin kuɗi, nan da watan gobe (Fabrairu), za ku fara karɓar N77,000 maimakon N33,000 da kuke karɓa a baya."

- Birgediya Janar Yusha'u Ahmed

Har ila yau, ya shawarci matasan masu yi wa ƙasa hidima da su guji duk wani hali ko ɗabi’a mara kyau da za ta iya kawo cikas ga burikan da suke son cimmawa a rayuwa.

Masu NYSC sun koka kan N33,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) sun miƙa kokensu ga gwmanatin tarayya kan alawus ɗin da ake biyansu.

Matasan sun koka da cewa N33,000 da gwamnati take biyansu sun yi kaɗan duba da yadda abubuwa suka carke a ƙasar nan.

Sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta tausaya musu ta fara biyan N77,000 da ta yi musu alƙawari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng