Hotuna da bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar jarumin kwallon kafa, Ahmed Musa

Hotuna da bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar jarumin kwallon kafa, Ahmed Musa

  • Abokan wasan Ahmed Musa na kulob din Fatih Karagümrük da ke kasar Turkiyya sun nuna masa soyayya yayin da yayi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 29
  • Kyaftin din na Super Eagles ya wallafa wani bidiyonsa tare da abokan wasan nasa wadanda suka shasshafa masa kek a fuska
  • Musa ya koma kulob din ne a lokacin rani bayan ya shafde dan wani lokaci da kulob din Kano Pillars na Najeriya a farkon shekarar

Abokan wasan kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa wanda ya cika shekaru 29 a ranar 14 ga watan Oktoba na kulob din Fatih Karagümrük da ke kasar Turkiyya sun shirya masa biki na musamman domin wannan rana, KemiFilani ta rahoto.

Dan wasan na Najeriya wanda ya shafe dan gajeren lokaci tare da Kano Pillars a farkon wannan shekarar bayan barin kungiyar Al Nassr ta Saudiyya ya ci gaba da birge sabuwar kulob dinsa.

Kara karanta wannan

An biya dan Najeriya diyyar N17m bayan abokin aikinsa ya kira shi da goggon biri a Ireland

Hotuna da bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar jarumin kwallon kafa, Ahmed Musa
Hotuna da bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar jarumin kwallon kafa, Ahmed Musa Hoto: ahmedmusa718
Asali: Instagram

Wani bidiyo da ke yawo a yanzu a kafafen sada zumunta ya nuna cewa Musa, wanda shine dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a Najeriya da kwallaye hudu, yana da tarin masoya a kulob dinsa.

An gano Musa wanda ke rike da kek yana ta murmushi yayin da abokan wasansa na Fatih Karagümrük suke tafa masa inda shi kuma ya hure wutar kendir na jikin kek din.

Yayin da wasu daga cikin 'yan wasan ke yi masa tsiya, wasu kuma suna ta bugunsa a sassa daban-daban na jikinsa ciki har da kansa yayin da duk suka taya tauraron raya wannan rana ta musamman.

Musa ya yi martani:

“Ba zan iya gode maku ba. Ga sakonni, kiraye-kiraye, addu’o’i da kyaututtukanku, ina godiya. A kullun za mu sami dalilan yin murna. Nagode da kuka sanya ranar zagayowar haihuwana ta zama ta musamman.”

Kara karanta wannan

Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya

Bidiyon Ahmed Musa yana kyautar kudi ga wasu tsala-tsalan ‘yan mata yayin da yake tuka motar G Wagon na N100M

A gefe guda, mun kawo cewa Ahmed Musa ya nuna karamcinsa ga wasu ‘yan mata yayin da yake tuka motarsa kirar G Gagon inda tsohon dan wasan na Leicester ya yi musu kyautar kudi.

‘Yan matan sun kasance a cikin keken adaidaita sahu lokacin da suka hango Ahmed Musa yana tuka motarsa ta G Wagon wanda kudinta ya kai naira milyan 100, sannan sai suka fara yi wa kyaftin din na Super Eagles kirari.

A cikin bidiyon da jakadiyan_arewa_tv ta wallafa a Instagram an jiyo yan matan suna shewa tare da neman ya sauke gilashin, sannan an jiyo wata cikinsu tana ihun kudi zai bamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel