Bidiyon Ahmed Musa yana kyautar kudi ga wasu tsala-tsalan ‘yan mata yayin da yake tuka motar G Wagon na N100M

Bidiyon Ahmed Musa yana kyautar kudi ga wasu tsala-tsalan ‘yan mata yayin da yake tuka motar G Wagon na N100M

  • Ahmed Musa ya yi kyautar kudi ga wasu ‘yan mata da suka jinjina masa a yayin da yake tuki
  • Tsohon dan wasan na CSKA Moscow yana tuka motarsa kirar G Wagon lokacin da ya hango yan matan a cikin adaidaita sahu
  • Ana sa ran Musa zai buga wa Super Eagles wasan da za su yi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Ahmed Musa wanda shine kaftin na Super Eagles ya nuna karamcinsa ga wasu ‘yan mata yayin da yake tuka motarsa kirar G Gagon inda tsohon dan wasan na Leicester ya yi musu kyautar kudi.

‘Yan matan sun kasance a cikin keken adaidaita sahu lokacin da suka hango Ahmed Musa yana tuka motarsa ta G Wagon wanda kudinta ya kai naira milyan 100, sannan sai suka fara yi wa kyaftin din na Super Eagles kirari.

Kara karanta wannan

Ta zub da hawayen farin ciki yayinda mijinta yayi mata kyautar Tsaleliyar mota Venza matsayin tukwicin nakuda

Bidiyon Ahmed Musa yana kyautar kudi ga wasu tsala-tsalan ‘yan mata yayin da yake tuka motar G Wagon na N100M
Bidiyon Ahmed Musa yana kyautar kudi ga wasu tsala-tsalan ‘yan mata yayin da yake tuka motar G Wagon na N100M
Asali: UGC

A cikin bidiyon da jakadiyan_arewa_tv ta wallafa a Instagram an jiyo yan matan suna shewa tare da neman ya sauke gilashin, sannan an jiyo wata cikinsu tana ihun kudi zai bamu.

A nashi bangaren, an gano sanda Ahmed Musa ya kalle su sannan ya dage gilashin motarsa kafin ya ba su kyautar kudi inda ya tafi ya bar matan cikin farin ciki.

Kalli bidiyon a kasa:

Ko shakka babu cewa Ahmed Musa yana daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya mafi kudi idan aka yi la’akari da abin da dan wasan mai shekaru 28 ya tara ta kwallon kafa.

Tsohon dan wasan na Kano Pillars ya kuma kasance masoyin tsadaddun ababen hawa duba ga manyan motocin da ke a garejinsa.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Ahmed Musa wanda a halin yanzu ya buga wa Super Eagles wasanni 98 yana hanyar kaiwa 100 kuma mai yiwuwa ya karya tarihin Joseph Yobo da Vincent Enyeama na wasanni 101.

Ana sa ran dan wasai zai isa sansanin Super Eagles a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, don buga kwallo biyu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel