Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya

Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya

  • Femi Adesina, hadimin shugaban kasa, ya caccaki wasu ‘yan Najeriya wadanda ke yada jita-jitar cewa an canja Shugaba Buhari da Jibrin na Sudan
  • Adesina, wanda ya kasance mai ba shugaban kasar shawara na musamman a kafofin watsa labarai, ya bayyana cewa abun bakin ciki ne cewa wasu mutanen sun yarda da karairayin
  • A cewarsa, ‘yan Najeriya sun yi matukar farin ciki lokacin da shugaban kasar ya dawo kasar bayan wasu watanni a Landan

Aso-Rock, Abuja - Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin labarai, Femi Adesina ya sake martani kan jita-jitan da aka ta yadawa game da ubangidansa lokacin da yake jinya a shekarun baya.

Legit.ng ta rahoto cewa Adesina ya ce wauta ne yarda da cewa shugaban kasar ya mutu sannan aka sauya shi da Jibrin daga kasar Sudan.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya
Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya Hoto: Sallau Buhari.
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Alhamis, 14 ga watan Oktoba, Adesina ya tuna da lokacin da suka yi da Buhari a 2017 lokacin da shugaban na Najeriya ya gane shi.

Ya ce:

“Na tuna da wannan rana a watan Agusta 2017, lokacin da shugaban kasar ya dawo kasar daga hutun jinya. Daga watan Janairu na wannan shekarar, ya kasance a waje da cikin kasar na wasu lokuta, amma ya shafe makonni da watanni a wajen kasar, yana kula da lafiyarsa. Sannan a karshe, a ranar 19 ga watan Agusta, sai ya dawo gida, cikin nasara.
“Mun kasance a filin jirgin sama don tarbansa, na sha fadar wannan labarin, don watsi da sakarcin cewa wani Jibril ne na Sudan ya dawo, amma ba Buhari ba. ‘Yar tsohon shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin, Za ta yi aure. Sai na halarci daurin auren na coci da liyafar bikin, na kasance sanye da shigar Yarbawa na babbar riga da hula iri daya. Kai tsaye daga wajen taron, na je filin jirgi don shiga sahun masu maraba da Shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021

“Mu manyan hadimai mun jeru don tarbar shugaban kasar yayin da yake sauka daga jirgin. Sannan ya dunga musabaha da kowani mutum, yana ta barkwanci, kamar yadda yake a al’adarsa. Da ya zo kaina, sai ya ce, “Adesina, wannan itace shiga mafi kyau da na taba gani kayi.” Sai dukka muka yi dariya.”

Hadimin Shugaban kasar ya ci gaba da cewa:

“Jibril na Sudan? Ta yaya ya san nine Adesina? Ta yaya zai san yadda na saba yin shiga? Sakarci, na sake fadi. Amma wannan wani sashi ne, ba labarin da nake son bayarwa don marawa batun da ke kasa baya ba.
“Mun shiga ababen hawar a jere, sannan jerin gwanon motocin suka tashi. Wannan shine tafiya mafi tsawo da na gani daga filin jirgi zuwa cikin gari. Daga Ina suka zo? Kamar dorawa, sun taru a hanyar, lokuta da dama suka tursasa jerin motocin rarrafe. Ban san cewa mutane da yawa haka suna zama a garuruwan Da ke hanyar filin jirgin ba."

Kara karanta wannan

An biya dan Najeriya diyyar N17m bayan abokin aikinsa ya kira shi da goggon biri a Ireland

Duk wanda yace Buhari ya gaza tantirin makaryaci ne, Femi Adesina

A wani labarin, Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa gwamnatin maigidansa bata gaza ba saboda tayi kokari a wasu wurare.

A hirar da yayi a shirin 'Politics Today' na ChannelsTV, Adesina yace duk wanda yace Shugaba Buhari ya gaza tantirin makaryaci ne.

Zaku tuna cewa Buhari ya dane mulki ne kan alkawura uku - Magance matsalar tsaro, yaki da rashawa, da kuma farfado da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel