Albashin ma'aikata
Gwamnatin tarayya ta gaza biyan ma’aikata albashinsu na watan Disamba kafin bikin Kirsimeti, hakan ya sa sun yi bikin cikin rashin farin ciki da walwala.
Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya amince da kyautar kudi na karshen shekara ga ma’aikan gwamnati a jihar a fadin matakai daga N20,000 zuwa N100,000.
A ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, Gwamna Francis Nwifuru ya amince da N100,000 a matsayin kyautar kirsimeti ga ma’aikatan jihar Ebonyi, harda buhun shinkafa.
Gwamna Umar Bago na jihar Niger ya ba da hutun kwanaki bakwai ga ma'aikatan jihar saboda bikin Kirsimeti tare da ware abinci don raba wa al'umma.
Gwamnatin jihar Cross River ta amince da tsawaita hutu ga ma’aikatanta. An fara hutun kuma ana sa ran ma’aikata za su koma bakin aiki a shekara mai zuwa, 2024.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya amince da N100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga ma'aikatan gwamnatin jihar. Kwamishinansa ya tabbatar da hakan.
A safiyar Lahadi aka fara jin cewa daga yau za a tafi yajin-aiki a Najeriya. Wannan sanarwa da ake ta yadawa karya ce kacokam kuma jama’a su yi watsi da ita.
Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya da jihohi suka ki biyan karin albashi da alawus na ma'aikata da aka alkawarta.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da karin N35,000 a albashin ma'aikatan gwamnatin jihar, da alawus na kashi 50% na albashin Disamba.
Albashin ma'aikata
Samu kari