Murna Yayin da Tinubu Ya Fara Biyan Albashin Ma’aikata da Aka Rike

Murna Yayin da Tinubu Ya Fara Biyan Albashin Ma’aikata da Aka Rike

  • Ma'aikatan tarayya na cikin farin ciki yayin da gwamnatin tarayya ta saki albashinsu da aka rike
  • A ranar Laraba, ma'aikatan gwamnati da ke bin albashin watan Nuwamba sun samu alat sannan sun sanar da manema labarai
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnati ta tantance ma'aikata 4,081 cikin 17,000 da tun farko aka cire su daga tsarin IPPIS

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fara biyan ma'aikatan gwamnati albashinsu na watan Nuwamba.

Tinubu ya amince da biyan albashin Nuwamba
Murna Yayin da Tinubu Ya Fara Biya Albashin Ma’aikata da Aka Rike Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ma'aikata sun cika da murna yayin da Tinubu ya amince da biyan albashin da aka rike

Ma’aikatan da gwamnatin tarayya ta hana su albashin su da farko saboda matsalar IPPIS sun fara samun alat na albashin watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Farin ciki yayin da gwamnan PDP ya sanar da ranar biyan albashin watan 13

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ma'aikatan gwamnati da dama sun tabbatarwa jaridar The Punch da hakan a Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa ma’aikatan gwamnati 2,000 ne gwamnati ta hana su albashin watan Nuwamba na 2023 sakamakon matsala a tsarin IPPIS.

Sai dai kuma, a ranar Laraba, wata babbar ma'aikaciyar gwamnati wacce ta tabbatar da samun albashinta ta ce:

"Alat din ya shigo yan mintuna da suka gabata. Ina farin cikin sanar da ku cewa an biya albashina na watan Nuwamban 2023 . Haka abun yake a bangaren sauran yan ofis dina."

Wani ma'aikacin gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: "Da gaske ne, an biya mu yanzun nan."

Wani abin sha'awa, ma'aikatan gwamnati da aka cire daga tsarin IPPIS, yanzu an sake shigar da su cikin lissafin albashin gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan tarayya 2,000 sun rasa albashin watan Nuwamba, an gano dalilin hakan

NLC ta magantu kan karin albashi

A wani labarin, mun ji cewa ganin yadda rayuwa ta ke kara wahala, kaya suka yi tsada a kasuwanni, kungiyar NLC ta ce dole sai an yi la’akari da wadannan.

Kafin a tsaida magana a game da abin da zai zama mafi karancin albashi, shugabannin NLC sun ce dole a duba yadda ake rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel