Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Sanya Yan Fansho Kuka Yayin da Ya Cika Musu Alkwarin da Ya Dauka, Ya Koka

Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Sanya Yan Fansho Kuka Yayin da Ya Cika Musu Alkwarin da Ya Dauka, Ya Koka

  • Gwamna jihar Kano, Abba Kabir ya cika alkawarin da ya dauka na biyan ‘yan fansho a jihar Kano
  • Gwamnan ya kaddamar da fara biyan kudaden ne a yau Asabar 2 ga watan Disamba a gidan gwamnati
  • Abba ya ce gwamnatin da ta shude ta bar musu basuka masu tarin yawa har na biliyan 48 na ma’aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kaddamar da biyan kudaden giratuti ga ma’aikata dubu biyar a jihar.

Abba Kabir ya ware naira biliyan 6 don bai wa ma’aikatan hakkinsu tare da wadanda su ka mutu a lokacin da su ke aiki, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Abba Kabir na Kano ya kaddamar da biyan kudaden fansho a Kano
Gwamna Abba Kabir ya cika wa 'yan fansho alkawarin da ya dauka. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Yaushe aka fara biyan fansho a Kano?

An gudanar da bikin kaddamar da biyan kudaden ne a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar a yau Asabar 2 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke jawabi, Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatar da biyan ma’aikata hakkokinsu.

Ya ce gwamnatinsa ta gaji tulin basukan ma’aikata daga tsohuwar gwamnatin da ta shude, cewar Daily Trust.

Ya kara da cewa tulin basukan sun hada da fansho na ma’aikatan da kuma wadanda su ka mutu a bakin aiki.

Wane damuwa gwamnan Kano ya nuna?

Ya ce:

“Ku na da labarin cewa tsawon shekaru takwas gwamnatin baya bata biya basukan ‘yan fansho ba amma ana cire kudade.
“Mun yi alkawarin biyan dukkan wadannan basuka kuma Alhamdulillah a yau mun cika wannan alkawari duk da wasu bukatu.”

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na Kano zai faranta ran tsofaffin ma’aikata, an tsaida ranar fara biyan kudin giratuti

Abba Kabir ya ce za a ci gaba da biyan kudaden da su ka kai biliyan 48 inda ya shawarci masu cin gajiyar da su yi amfani da kudaden yadda ya dace.

Shugaban kungiyar ‘yan fansho, Kwamred Godwin Abumisi wanda ya samu wakilcin Kwamred Abdullahi Tsoho ya yaba wa gwamnan da irin wannan taimako.

Ya ce biyan kudaden ya zo a dai-dai lokacin da wasu ‘yan fansho ke cikin wani mummunan yanayi.

Gwamna Abba Kabir zai biya ‘yan fansho

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ware naira biliyan shida don biyan kudaden ‘yan fansho a Kano.

Gwamnan ya ce a cikin kudaden har ila yau za a biya giratuti na wadanda su ka mutu yayin da su ke aiki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel