Kano: Sabon Shugaban Ma’aikata da Abba Kabir Ya Nada Ya Shiga Ofis da Kafar Dama, Ya Yi Gargadi

Kano: Sabon Shugaban Ma’aikata da Abba Kabir Ya Nada Ya Shiga Ofis da Kafar Dama, Ya Yi Gargadi

  • Kwanaki biyu bayan nadin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin Kano, Musa Abdullahi ya kama aiki ba kama hannun yaro
  • Musa ya zama sabon shugaban ma’aikatan jihar ne a ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba da sahalewar Gwamna Abba Kabir
  • Sabon shugaban ya gargadi ma’aikata da su sauya tunaninsu kan zuwa wurin aiki a latti inda ya ce dole su kasance a ofis karfe takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Sabon shugaban ma’akatan gwamnatin jihar Kano, Musa Abdullahi ya fara aiki a ofishinsa.

Gwamna Abba Kabir ya nada Alhaji Musa Abdullahi mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar a wannan mako.

Sabon shugaban ma'aikatan Kano ya gargadi ma'aikata kan aiki
Sabon shugaban ma'aikatan Kano ya shiga ofis. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Yaushe aka nada sabon mukamin a Kano?

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada babban mukami a gwamnatinsa, an bayyana sunansa

Nadin na Musa na zuwa ne bayan tsohon shugaban ma’aikatan, Alhaji Usamn Bala ya yi murabus a mukaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kabir ya ci gaba da aiki da shi tun bayan hawanshi karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, cewar The Nation.

Jim kadan bayan ya karbi ragamar ofishin daga tsohon shugaban ma’aikatan, Musa ya godewa gwamnan bisa wannan dama.

Musa ya ce ya karbi ragamar ofishin da zuciya daya kuma zai yi dukkan abin da ya da ce don tabbatar da abin da ake nema.

Wane gargadi Musa ya yi wa ma'aikata?

Sabon shugaban ma’aikatan shi ne wanda aka nada na 13 inda ya yi alkawarin fara wa daga tushe don kawo sauyi a jihar.

Ya kuma yi alkawarin kawo sabbin dabaru da hikimomi don ci gaba da inganta ofishin kamar yadda ta ke a baya, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan ya sake fallasa yadda aka kai Najeriya gargara kafin zuwan Tinubu

Mista Musa ya gargadi ma’aikata da su daura damarar kawo sauyi don ba zai yi soko-soko da aikin gwamnati ba.

Ya gargade su kan zuwa wurin aiki da wuri inda ya ce dole ma’aikaci ya kasance a bakin aiki tun karfe takwas na safe.

Gwamna Abba na nada sabon shugaban ma’ikata

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada sabon shugbaban ma’aikatan gidan gwamnatinsa.

Abba ya amince da nadin Alhaji Musa Abdullahi a matsayin sabon shugaban a ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba.

Nadin Musa na zuwa ne bayan murabus da tsohon shugaban ma’aikatan, Alhaji Bala Usman ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel