Gwamna Lawal Ya Sake Tono Zunzurutun Bashin da Tsoffin Gwamnoni Biyu Suka Bar Masa Tun Daga 2015

Gwamna Lawal Ya Sake Tono Zunzurutun Bashin da Tsoffin Gwamnoni Biyu Suka Bar Masa Tun Daga 2015

  • Gwamna Dauda Lawal ya bayyana makudan kuɗin da ma'aikatan da suka yi ritaya suka biyo gwamnatin Zamfara bashi
  • Ya ce bayan hawansa kan madafun iko ya ɗauki matakai kuma ya yi alkawarin fara biyan gratuti da alawus din yan fansho
  • Lawal ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa ta rage ma'aikatu da kwamishinoni domin rage kashe-kashen kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya sake bankaɗo wasu zunzurutun kuɗin gratuti da alawus din yan fansho da waɗanda suka yi ritaya suke biyo gwamnatin jihar bashi.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Ma'aikatan da suna aje aiki sun biyo bashin N13.6bn a Zamfara, Gwamna Lawal Hoto: Dauda Lawal Dare
Asali: Facebook

Lawal ya ce gwamnatin jihar na da bashin sama da naira biliyan 13.6 na kudaden gratuti da alawus-alawus na fansho da za a biya wadanda suka yi ritaya daga 2015 zuwa yau.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe gawurtaccen ɗan bindigan da ya hana jama'a zaman lafiya a arewa

Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar manyan sakatarorin Najeriya da suka yi ritaya reshen jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels tv ta tattaro rahoton cewa taron ya gudana ne a Gusau, babban birnin jihar Zamfara da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wane mataki zai ɗauka don biyan wannan bashin?

Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin cewa a karkashin gwamnatinsa, za a fara biyan haƙƙoƙin gratuti da alawus din yan fansho ga waɗanda suka gama aiki.

A cewarsa, biyan waɗannan basussuka zai kara inganta walwala da rayuwar ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.

A cewar Gwamna Lawal, bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da matakai masu kyau domin rage tsadar harkokin mulki.

Daga cikin matakan Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta rage yawan ma'aikatu da kwamishinoni zuwa 18 kaɗai, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Ya ce ya kafa kwamiti tare da ɗora musu nauyin tantance ma'aikata na dukkan ma'aikatu domin tabbatar da ainihin adadinsu da nufin inganta ayyukansu.

Majalisar ta gyara kwamitoci 27

A wani rahoton na daban Majalisar wakilan tarayya ta yi gyara a shugabancin kwamitoci 27 yayin da aiki ya fara kankama kan kasafin kuɗin 2024.

Tajudeen Abbas ya karanto sabbin ciyamomin kwamitocin da mataimakansu biyo bayan tsige wasu yan majalisa da kotu ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel