NLC: Abin Gwamnatin Tinubu Za Ta Duba Wajen Yin Karin Albashin Ma'aikata a 2024

NLC: Abin Gwamnatin Tinubu Za Ta Duba Wajen Yin Karin Albashin Ma'aikata a 2024

  • Kungiyar ma’aikata a Najeriya watau NLC ta ce ya kamata a duba tsadar rayuwa a wajen yin karin albashi a 2024
  • Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce abubuwa sun yi tsada a yau don haka wajibi ayi la’akari da hakan kafin yanke albashi
  • Tun da Ibrahim Badamasi Babangida ya fito da tsarin tattalin arziki na SAP, Ajaero ya ce ake shan wahala a kasar nan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ganin yadda rayuwa ta ke kara wahala, kaya suka yi tsada a kasuwanni, kungiyar NLC ta ce dole sai an yi la’akari da wadannan.

Kafin a tsaida magana a game da abin da zai zama mafi karancin albashi, shugabannin NLC sun ce dole a duba yadda ake rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Tsaida Lokacin Fara Biyan Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata

Karin Albashin Ma'aikata a 2024
'Yan NLC na neman karin albashi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Albashi daidai da wahalar rayuwa - NLC

This Day ta rahoto kungiyar ‘yan kwadago da NLC ta na cewa za ta tabbata an duba wahalar da ake sha wajen yanke sabon tsarin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan kwadago sun ce jama’a sun shiga mawuyacin hali a sakamakon cire tallafin fetur, aka kuma bukaci dawo da ma'aikatan jihar Imo.

Shugaban NLC ya yi jawabi kan karin albashi

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya yi bayanin wahalar da ma’aikata su ke sha da ya halarci taron bude wata makaranta a garin Abuja.

Kwamred Joe Ajaero yake cewa ya zama wajibin gwamnatoci a kowane irin mataki su duba wahalar da mutane su ke sha yau a kasar nan.

A cewar shugaban na NLC, masu aikin gwamnati da ‘yan kwadago suna fama da talauci, tsadar rayuwa da sauran matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Yawan kuri'u ba shi ne kadai alamar nasara a zabe ba, cewar Doguwa

Dole sai ma’aikaci ya ji dadin aiki sannan Joe Ajaero yake ganin za kasa za ta cigaba. Jaridar The Cable ta kawo labarin nan a ranar Talata.

Sakataren NLC watau Emma Ugboaja ya yarda da Ajero wanda ya ce tun da aka kawo tsarin tattali na SAP ma’aikata su ke wahala a Najeriya.

Jawabin shugaban NLC, Joe Ajaero a kan albashi

"Yayin da mu ke jiran fara tattaunawa a kan mafi karancin albashi a 2024, muna neman hadin-kan duk masu ruwa da tsaki
Muna so mu yi amfani da wannan daman wajen cin ma matsaya a kan albashin da zai zo daidai da yanayin rayuwar da ake yi."

- Joe Ajaero

"Dole gwamnati ta karbo bashi" - Sanata

Ana da labari cewa Sanata Jimoh Ibrahim ya ce dole gwamnatin Bola Tinubu ta ci bashi idan ana so ayi ayyukan more rayuwa a kasar.

‘Dan siyasar ya ce Muhammadu Buhari bai iya kammala wata kwangilar $1bn ba sai dai kalaman Sanatan sun harzuka wasu ‘ya ‘yan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel