Aikin noma a Najeriya
Kayan abinci sun yi tsada a dalilin rashin samun taki, rashin kyawun noman damina, rufe iyaka da kokarin gwamnati ya sa musamman shinkafa za ta fi karfin talaka.
Manoma sun shiga tsahin hankali a wasu ƙauyuka akalla 15 da ke jihar Taraba biyo bayan ayyukan 'yan bindiga wanda ya tilasta musu hakura da amfanin gonakinsu.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanar da karbo rancen kuɗaɗe har dala miliyan 163 domin bunƙasa noman alkama a ƙasa baki ɗaya. Kashim Shettima ne ya bayyana.
Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta ce za a tafka mamakon ruwan sama a Kano da Sakkwato, akasin Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Akwa Ibom, Abia, Ebonyi.
Yayin da barayi su ka yi yawa yanzu wurin satar amfanin gona, wasu manoma sun bayyana yadda su ke biyan kudi tare da kwana a gonaki don gudun satar kayan gona.
Za a ga tsadar abinci, buhun shikafa zai kuma tsada a kasuwa. ‘Yan kasuwan da ke Arewa a karkashin NACCIMA sun fara ankarar da al’umma kan halin da ake ciki
Gwamnatin Dikko Umaru Radda za ta raba 30, 000 na abinci. Bayan Gwamnan Katsina da zai raba abinci, an karya taki a Jigawa, mota za tayi sauki a jihar Legas.
Najeriya na kara fadawa matsala yayin da ake samun karuwar samun wasu abubuwan da ke tashi. Yanzu haka an ce wata kwayar cuta ta bullo a kasar tana kama kubewa.
JIhohi biyar ne hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana cewa sun fi kowace jiha a Najeriya sayen kayayyakin abinci da tsada. Cikin jihon akwai jihar Kwara.
Aikin noma a Najeriya
Samu kari