Kamfanonin Arewa Sun Tsaida Aiki, Watakila Shinkafa Za Ta Kara Tsada a Kasuwa

Kamfanonin Arewa Sun Tsaida Aiki, Watakila Shinkafa Za Ta Kara Tsada a Kasuwa

  • ‘Yan kasuwan Arewa a karkashin NACCIMA sun fara ankarar da al’umma kan halin da ake ciki
  • Shugaban kungiyar NACCIMA ya fadawa ‘yan jarida su na fama da karancin kayan amfanin gona
  • Tasirin da za a gani na gaggawa ba zai wuce tsadar shinkafa ba, hakan zai kara jefa jama’a a yunwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Kungiyar NACCIMA ta ‘yan kasuwan yankin Arewa ta ce kamfanonin casar shinkafa sun fara dakatar da aiki a Jihar Kano a halin yanzu.

Rahoton The Cable ya nuna abin da ya jawo tsaida ayyukan kamfamonin shi ne karancin samfarera shinkafada ake fuskanta domin sarrafawa.

Shugaban NACCIMA, Dalhatu Abubakar ya fadawa manema labarai rashin samfarera zai yi sanadiyyar tsadar buhun shinkafa a kasuwannin kasar.

Shinkafa
Gonar shinkafa a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A bayanin da ya yi a ranar Litinin, ‘dan kasuwan ya ce ya zama dole a dauki matakin da ya kamata domin a gujewa fadawa matsalar rashin abinci.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lamarin zai iya yin kamari domin kayan amfani su na nema su kare a daidai lokacin da mutane ke ta faman addu’ar rokon ruwa a wasu garuruwa.

Halin da kamfanoni su ka shiga

Shugaban kamfanin casar shinkafar na Al-Hamsad ya ce a wurare da-dama ana rage ma’aikata ko dai akalla a rage awannin da ake yi a wurin aiki.

Jaridar ta ce Abubakar ya nemi gwamnatocin tarayya da na jihohi su kawo agaji ta yadda manoma za su iya yin shuka a kowane lokaci a shekara.

A halin yanzu wasu kamfanonin da ke casar shinkafa, su na sayo ton kan N400, 000.

Dr. Sanusi Y. Muhammad malamin jami'a ne kuma kwararre a harkar noma, ya fadawa Legit.ng Hausa cewa ana fama da karancin samfarera.

Masanin wanda ya ke aiki da kamfanin casar shinkafa ya ce tsadar takin zamani a bara, rashin tsaro da yawaitar kamfanonin su na cikin sanadi.

Kara karanta wannan

Dillalai Sun Tsaida Karin Kusan N100, Litar Fetur Za Ta Iya Komawa N680-N720

Yawaitar kamfanonin casar a lokacin da ake cikin rashin zaman lafiya a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya zai kara jawo tsadar shinkafar.

Tinubu ya ce a raba abinci

Rahoton da aka samu kwanaki ya nuna farashin kayayyakin abinci zai faɗi warwas, watakila hakan zai jawo jama'a su rage kukan da su ke yi.

Wannan na zuwa ne yayin da majalisar NEC ta umarci hukumar NEMA ta gaggauta fito da hatsi ta rabawa jihohi domin karya farashin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel