Jonathan Ya Samu Babban Mukami A Afirka, An Bayyana Mukami Mai Muhimmanci Da Ya Samu

Jonathan Ya Samu Babban Mukami A Afirka, An Bayyana Mukami Mai Muhimmanci Da Ya Samu

  • Tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan ya samu babban mukami a Afirka bayan ayyukan da ya yi wa kasar daga 2015 zuwa 2019
  • An nada Jonathan a matsayin jakadan gidauniyar fasahar noma ta Afirka (AATF)
  • A bangare guda, an yi wa tsohon shugaban kasar nadin ne saboda ayyukan da ya yi na tallfawa bangaren noma a nahiyar

Wani rahoto d jaridar Daily Trust ta fitar ya ce gidauniyar African Agricultural Technology Foundation ta nada tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Goodluck Ebele Jonathan a matsayin jakadar fasahar noma.

Direkta Janar na AATF, Dr Canisius Kanangire, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Juma'a, 2 ga watan Disamba a Abuja bayan taro da tsohon shugaban kasar a Yanagoa, jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Hukumar Sojojin Kasa Tace Zata Canja Fasalin Kai Hare-Hare A Fadin Nigeria

Goodluck Jonathan
Jonathan Ya Samu Babban Mukami A Afirka, An Bayyana Mukami Mai Muhimmanci Da Ya Samu. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Mr Jonathan, wanda shine shugaban kasar Najeriya daga 2010 zuwa 2015, an ce shine jagaba a bangaren habbaka harkokin noma a nahiyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da ya ke karbar nadin, ya ce a matsayinsa a matsayin tsohon shugaban kasa, abin da ya sa a gaba shine samar da tsaro na abinci da inganta rayuwar mutanen Afirka, rahoton jaridar Leadership.

Goodluck Jonathan a matsayin dan kishin nahiyar Afirka

Daraktan na AATF ya ce ana iya ganin sadaukarwar da Jonathan ya yi na bunkasa aikin gona a nahiyar ta ajandar kawo sauye-sauye da ya yi a bangaren noma lokacin yana shugaban Najeriya.

Ya kara da cewa:

"AATF tana alfahari da samun tsohon shugaban kasar a matsayin Jakadanmu, wanda aikinsa zai kara habaka kokarin da ake yi na inganta harkar noma."

Jonathan: Dole Mu Tabbatar Da Najeriya Kafin Samun Shugaban Kasa

Kara karanta wannan

Babban Rashi, A Yayin Da Tsohon Shugaban Kasa Mai Karfin Fada A Ji, Ya Mutu Yana Da Shekara 96

A wani rahoton, a yayin da babban zaben shekarar 20223 ke karatowa, tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Jonathan, ya janyo hankalin jam'iyyun siyasa su kaucewa tada zaune tsaya, yana mai cewa sai da Najeriya sannan a samu shugaba.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a babban birnin tarayya Abuja yayin taron zaman lafiya na shekarar 2022 da Goodluck Jonathan Foundation ta shirya.

Dr Jonathan ya bukaci masu rike da mulki su kare martabar Najeriya kasancewarta babban kasa a nahiyar Afirka da kamata saura su rika koyi da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel