Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

  • Gwamnatin Dikko Umaru Radda PhD za ta raba buhuna fiye da 30, 000 na abinci a jihar Katsina
  • Gwamnan jihar Legas ya rage farashin hawa motocin haya saboda a iya saukaka kudin zirga-zirga
  • Babajide Sanwo Olu zai samar da karin motocin haya da nufin jigilar ma’aikata zuwa wurin aiki

Katsina - Ganin halin da al’umma su ka shiga a sakamakon janye tallafin man fetur da tashin farashin kaya, gwamnatoci sun fara daukar matakai.

Gwamnatin jihar Katsina ta waiwayi talaka kamar yadda wata sanarwa ta bayyana daga ofishin Mai taimakawa Gwamna Dikko Umaru Radda.

A shafinsa na Twitter, Isah Miqdad ya shaida cewa gwamnati za ta raba kayan abinci kyauta a garuruwa sakamakon wahalar da talakawa ke yi.

Sabon Gwamna
Wasu Gwamnonin Jihohi Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Jawabin Mai ba Gwamna shawara

"Domin rage radadin tattalin arziki da talakawa su ke fuskanta yanzu, a yau gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda (Gwagwaren Katsina) ya bada umarnin fito da buhuna 36, 100 na hatsi domin a raba a fadin mazabu 361 na jihar a kyauta.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Isa Miqdad Jr.

Sanarwar ta fito ne a farkon makon nan, sai dai zuwa yanzu ba mu da masaniyar inda aka kwana wajen rabon kayan abincin ga talakawan da ke jihar.

Tausayin Gwamnan jihar Katsina

A wani bidiyon na dabam, an ga irin tausayin Mai girma Dikko Umaru Radda, yayin da ya tsaya duba wata Baiwar Allah da ta ke jinya a wani kauye.

Gwamnan ya yi alkawarin daukar dawainiyar matar, ya ce za ayi mata maganin ciwon ta.

Tsarin gwamnatin jihar Legas

A wani jikon a Legas, Gwamnatin Babajide Sanwo Olu za ta rage kudin wasu motocin haya da 50% ganin cire tallafin man fetur ya jawo farashi ya tashi.

Hadimin Gwamnan, Jibril Gawat ya fitar da jawabi a Twitter yana cewa daga Laraba za a sanar da rage 25% a kudin hawa rawayan motocin hayan jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Gwamnatin Legas ta kuma ce za a karo motocin haya domin jigilar ma’aikatan gwamnati.

A kowane Gwamna yana yin irin na shi kokarin na ganin ya sauwaka talakawa tsadar rayuwa, a Jigawa an ji yadda gwamnati ta karya kudin taki.

Tinubu ya canza tunani

Kwanakin baya aka ji labari gwamnatin tarayya za ta sake duba tsarin raba kyautar N8, 000 domin kawo sa’ida ga marasa karfi ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin tarayya za ta sanar da mutanen Najeriya daukacin tsarin tallafin da gwamnati za a kawo bayan an soke tsarin biyan tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel