Tsananin Tashin Kayan Masarufi Nasa Wasu Magidanta Tsallake Cin Abincin Rana ko Na Safe

Tsananin Tashin Kayan Masarufi Nasa Wasu Magidanta Tsallake Cin Abincin Rana ko Na Safe

  • Tashin farashin abinci, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, na ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya barazana
  • Lamarin da ya tilastawa iyalai su rage yawan abincin da suke ci, ko kuma su ringa tsallake cin abincin wani lokaci
  • Kayan masarufi a Nigeria na tashi kamar wautar daji, inda zaka siyi abu yanzu in ka dawo ya sheda ma ya tashi

Abuja: Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masana suka yi gargadin cewa har yanzu akwai barazana dan gane da illar ambaliyar ruwa ta afku a mafi yawan sassan kasar nan kan samar da abinci.

Masanan sun ce za a iya samun 'kamarin lamarin a cikin watanni shida masu zuwa.

Binciken da jaridar Daily Trust tayi ta gano akasarin iyalai suka koma cin abinci sau biyu maimakon uku a matsayin hanyar tinkarar lamarin, wasu kuma sun tilasta kansu rage abincin da suke ci dana ‘ya’yansu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Feleken Da Farashin Abinci

A Ikate da ke Surulere, a wajen birnin Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, Doris Nwachukwu, mai sayar da kayan abinci, ta ce ta ga yadda kwastomominta ke kokawa da tsadar kayayyaki a watannin da suka gabata.

“Shinkafa, garri, albasa, indomie, komai ya tashi akan farashi. Wasu sun ninka fiye da ninki biyu, wasu sun yi tashin gwaron zabi da adai 'kare-karen akan kowanne kaya,” inji ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A binciken da Daily Trust tai, ya nuna cewa garri, 'daya daga cikin kayan abinci a Najeriya da ake siyar da shi kan Naira 500 a watan Janairun bana a kan bokitin fenti, ya kai Naira 700 a watan Maris, sannan ya haura Naira 1,100. A halin yanzu dai bokitin fenti daya ana sayar da shi akan Naira 1,000.

Haka kuma buhun shinkafar gida mai nauyin kilogiram 50 ya tashi, inda a halin yanzu ake sayar da shi kan N36,000. A watan Janairu kuma an sayar da irin wannan adadin akan N27,000.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

“Amma yawancin kudaden shiga na masu siye ba su canza ba. Mutane na korafin rashin kudi idan sun zo syen kaya. Idan ka ce musu buhun shinkafa yanzu ya kai Naira 36,000 za su ce sun lissafa shi ne su akan Naira 30,000. sai kaga suna ta mamakin yadda ya tashi daga N30,00 zuwa N36,000 cikin kankanin lokaci.
“A wasu lokuta, abokin cinikayya na yanke shawarar ya fasa saya. Wasu da suka yi niyyar siyan kuwa sai dai su sai rabi ko kwata. Abin da muke gani ke nan yanzu,” in ji 'yar kasuwa Nwanchuku.

Spaghetti, wanda ke zama madadin shinkafa, itama ta tashi a farashin ta. Da Farashin kowace fakiti N150 zuwa N250, amma yanzu N350, yanzu kuma N450.

Ya Labarin Yake a arewa

A wani labarin kuma a Kano (Arewa maso Yamma), wani dan kasuwa mai suna Shuaibu Mahammad, wanda ke da karamin shago a Kasuwar singa, ya ce ya yi mamakin hauhawar farashin kayayyaki a kullum.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

Food Price
Tsananin Tashin Kayan Masarufi Nasa Wasu Magidanta Tsallake Cin Abincin Rana ko Na Safe Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce yanzu ya daina sayan kayan abinci da yawa saboda yadda jarinsa ya zama da kuma tsoron karma tashin kayyyaki yasa ya daina kasuwanci.

“Yanzu ina sayarwa ne mudu-mudu sabida 'yan uwana talakawa su zo su ringa auna".
“Farashin yana ci gaba da 'karuwa kowace rana. Hakika wannan yana shafar mu. Yawancin ƴan kasuwa da yawa sun na shan wahala wajen ciyar da iyalansu.

Wata bazawara kuma mahaifiyar ‘ya’ya hudu Habiba Sama’ila ‘yar shekara 40, ta ce tashin farashin kayan masarufi, tare da mutuwar mijinta a ‘yan shekarun da suka gabata, ya tilasta mata barin duk wata sana’a, saboda duk jarinta ya kare wajen ciyarwa. iyali.

"Al'amura suna faruwa a kowace rana. Ba mu kuma tunanin wani abu sai abinci, kuma 'kudin sa sai 'karuwa yake. Mutane irina da ba su da mai tallafa musu suna cikin matsala,” in ji ta.

Hauhawar Farashin Kayayyakin Masarufi

Kara karanta wannan

Kada Kuji Tsoron Za'ai Fari Ko Karancin Abinci, Mun Tanadi Filayen Noma - NALDA

Abin da ke faruwa a Ikate (Lagos) da Singa (Kano) lamari ne da ya zama ruwan dare gama gari a Najeriya yayin da farashin kusan duk wasu kayayyakin gida da aka sani ya tashi.

Wannan hauhawar farashin ya cutar da talakawa, in ji Dokta Muda Yusuf, shugaban cibiyar kasuwanci mai zaman kanta kuma tsohon darakta-janar na kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas.

“Kamar yadda kuke gani, abubuwan da iyalai ke amfani dashi a gidajensu yanzu ya karu da da kashi 70 cikin 100, wasu ma ya kai kashi 80 cikin 100 saboda dole ne ka ciyar da iyalinka,”

Yusuf ya yi nuni da cewa, 'daya daga cikin abubuwan da ke haifar da hakan shi ne 'karuwar fatara a Najeriya, inda mutane da dama shiga 'kangintalauci.

“Idan har za a yi maganin wannan matsalar ta talauci, sai an magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, ta yadda talaka zai samu akalla ya sayi wani abu a cikin sauki da zau iya sarrafawa". .

Kara karanta wannan

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

Dalilan hauhawar farashi

Hauhawar farashin kayayyaki ya samo asali ne daga abubuwa da dama, na gida da waje, in ji Dokta Yusuf.

Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban dalilin tashin farashin kayayyakin abinci, sai kuma tabarbarewar ababen more rayuwa da suka hada da sufuri da wutar lantarki.

“Dalilin da ya sa abubuwa suka yi muni sosai a Najeriya shi ne rashin tsaro.
“Kusan kashi 90 cikin 100 na harkar noma, ana yi ta hanyar gargajiya, amma kuma ga yadda al’umma na karuwa". inji Dakta yusuf

Hukumar ta NBS ta dora alhakin hauhawar farashin kayayyaki da ake shigowa da su daga kasashen waje, sakamakon faduwar darajar kudin kasar nan.

Sai dai Yusuf ya ce:

"Farashin kayan abinci zai kara tashin gwauron zabi sabida tasirin ambaliyar ruwa da aka tafa".

Asali: Legit.ng

Online view pixel