Labari Mai Dadi Yayin Da Najeriya Da Ukraine Ke Shirin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Ta Noma

Labari Mai Dadi Yayin Da Najeriya Da Ukraine Ke Shirin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Ta Noma

  • Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cigaba da mayar da hankali wurin bunkasa aikin noma a kasar
  • A baya-bayan nan, gwamnatin kasar Ukraine ta nuna alamun cewa tana shirin amincewa da bukatar gina wurin ajiyar hatsi a Najeriya
  • Ana sa ran wannan hadin gwiwar zai bukasa tare da karfafa zumunci tsakanin kasashen biyu

Bisa alamu Najeriya da kasar Ukraine na daf da yin hadin gwiwa kan aikin noma a cikin yan makonni domin inganta da bunkasa cigaban noma a kasar ta Afirka ta Yamma.

Kamar yadda Ukrinform ta rahoto, gwamnatin Ukraine na shirin duba yiwuwar aiwatar da bukatar gwamnatin Najeriya na gina rumbu na ajiyar hatsi da wasu kayan abinci.

Buhari
Labari Mai Dadi A Yayin Da Najeriya Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Bunkasa Noma Da Ukraine. Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Gwamnatin na Ukraine ta bayyana wannan cigaban ne bayan wani muhimmin taro tsakanin Hukumar Noma ta kasa da Ministan Abinci Mykola Solskyi, Ministan harkokin kasashen waje na Najeriya Geoffrey Onyeama da Ministan Noma da Cigaban Karkara Mohammad Mahmood Abubakar.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Burtaniya ta gayyaci Atiku don wata ganawar sirri, an gano abin da suka zanta akai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da ya ke magana kan abin da aka tattauna a taron, an ambato Solskyi na cewa:

"Ukraine na son yin wannan aikin kuma a shirye ta ke ta duba bayanan."

An yi taron ne cikin ziyarar da Ministan Tsarin Noma da Ma'aikatar Abinci ya kawo kasashen Afrika.

Bangarorin biyu sun tattauna yiwuwar hadin kai da fadada harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, na gina cibiya ta zirga-zirga da musayar hatsi da kayan abinci.

Gwamnatin Tarayya ta fitar da N600bn domin tallagawa manoman Najeriya

A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 600 domin taimakawa manoma a fadin kasar.

Mallam Sabo Nanono, Ministan noma da raya karkara ne ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da shirin tallafawa manoma a birnin Kano.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa a bangaren watsa labarai shima ya tabbatar da hakan cikin wata wallafa da ya yi, yana mai cewa za a bada kudin ga manoma miliyan 2.4 daga cikin manoman da ke kasar saboda daukan dawainiyar ayyukan su.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai, Ya Nada Sabon Shugaban FHFL

Hakan ya dace da alkawurran da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi na mayar da hankali kan bunkasa ayyukan noma da tallafa wa manoma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel