Jihar Kwara Ce Kan Gaba a Jerin Jihohi 5 Da Suka Fi Fama Da Tsadar Abinci a Najeriya

Jihar Kwara Ce Kan Gaba a Jerin Jihohi 5 Da Suka Fi Fama Da Tsadar Abinci a Najeriya

  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana yadda yawancin magidanta ke ciyar da iyalinsu abinci da kyar da jibin goshi
  • Yayin da ‘yan Najeriya a wasu jihohin ke samun saukin sayan kayayyakin abinci, mazauna jihohi biyar na fuskantar akasin haka
  • Hakan na faruwa ne a lokacin da darajar naira ke ci gaba da kara tabarbarewa duk kuwa da hauhawar farashin kayayyakin da ake samu

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), a cikin rahotonta na baya-bayan nan game da farashin kayayyaki da ta fitar, ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 22.79% a watan Yunin 2023.

Hauhawar farashin kayayyakin da aka samu a watan Yuni, shine mafi girma a cikin sama da shekaru 17 da maki 0.38%, idan aka kwatanta shi da 22.41% na hauhawar farashin kayayyaki na watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Jihohin Najeriya 5 da suka fi fama da tsadar kayan abinci a Najeriya
Jerin jihohi 5 da suka fi fama da tsadar abinci a Najeriya. Hoto: Chimenx
Asali: UGC

Tsadar kayayyakin abinci a Najeriya

Hukumar ta NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki na shekara-shekara, ya karu da kashi 25.25%, inda ta ce akwai kuma yiwuwar karuwarsa a watanni masu zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa, hauhawar farashin kayan abinci da aka samu a Najeriya na watan Yunin 2023 ya fi na watan Mayu da kashi 2.40%, da kuma maki 0.21%.

Hakan na nufin cewa magidanta a Najeriya na kashe mafi yawan kudadensu wajen sayen kayan abinci irin su mai, burodi da hatsi, kifi, dankali, dawa, sauran abubuwa.

Jihohi 5 da suka fi fama da tsadar kayayyakin abinci a Najeriya

1. Kwara

Bayanan da hukumar ta NBS ta fitar a watan Yuni, ya nuna cewa jihar Kwara ce kan gaba wajen sayan kayayyakin abinci da tsada.

Bayanan sun nuna kayayyakin abinci a jihar, sun yi tashin gwauron zabi da kaso 30.80%.

Kara karanta wannan

Darajar Naira Ta Yi Kasa Yayin Da Hauhawar Farashi Ya Koma Kaso 22.7%, Na 11 Mafi Muni a Nahiyar Afirika

Hakan ya faru duk kuwa da irin kasar noman da jihar ke da ita, wacce ake iya shuka kayayyakin amfanin gona da yawa a cikinta.

2. Legas

Jiha ta biyu a jerin jihohi biyar da suka fi sayan kayayyakin abinci da tsada a Najeriya ita ce jihar Legas.

Rahoton da NBS ta fitar ya nuna cewa an samu hauhawar farashin kayan abinci a jihar da kaso 30.37% a shekarar da muke ciki.

3. Kogi

Jihar Kogi ce ta uku cikin jihohi masu sayan kayan abinci da tsada a Najeriya, wacce aka bayyana samun hauhawar farashi a cikinta da kasha 29.71% cikin dari.

Mazauna jihar na siyan kayayyakin abinci da tsada duk da kasar noma mai fadin gaske da Allah ya albarkaci jihar da ita.

4. Ondo

Jihar Ondo ma na daya daga cikin jihohin da ke da kasar noma, sai dai hakan bai hana ta zama ta hudu ba a jerin jihohin da suka fi sayan kayayyakin abinci da tsada.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Hukumar NBS ta ce an samu karuwar farashin kayan abinci a jihar da kashi 29.17% a watan Yunin da ya gabata.

5. Imo

Imo ce jiha ta karshe a jerin jihohi biyar da suka fi kowace jiha sayan kayayyakin abinci da tsada.

Hukumar NBS ta ce an samu hauhawar farashi a jihar ta Imo da kashi 28.04% a watan Yunin da ya shude.

Abubuwa takwas da ya kamata ku sani dangane da hauhawar farashi a Najeriya

A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan abubuwa takwas da ya kamata jama’a su sani dangane hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

A cikin rahoton, an yi duba da abubuwan da ke janyo hauhawar farashin da kuma hanyoyin da gwamnati za ta iya bi don magance shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel