Siyasar Najeriya
Gabannin babban zaben 2023, jam’iyyar APC na jan ragamar jihohi 21 a Najeriya, yayin da PDP mai adawa ke da jihohi 14. APGA kuma na da jiha guda daya kacal.
Sanata Orji Kalu, bulaliyar majalisar dattawan Najeriya ya ce sauya fasalin naira ba zai kawo cikas ga nasarar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ba.
Kotun daukaka kara mai zama a Adi Ekiti babban birnin jihar Ekiti ta kori karar da ɗan takarar Social Democratic Party, Segun Oni, ya shigar gabanta kan zaben.
Yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi, an ga 'yan kasuwa na ci gaba da karbar tsoffin kudade a wurin taron gangamin kamfen dan takar Tinubu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Alliance (AA), Hamza Al-Mustapha ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ai ya janyewa Atiku Abubakar takara.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya gargadi 'yan Najeriya kan zaben dan takarar shugaban kasa saboda shugabannin addinansu sun nemi su yi haka.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa cikin ruwan sanyi zai kayar da abokin hamayyar sa, na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu wani gagarumin tagomashi, malaman addini 100 sun koma bayan sa a jihar Rivers
A yayin da zaɓen 2023 yake ƙara ƙaratowa, ƴan takara masu neman kujeru daban-daban sun rigamu gidan gaskiya. Rasuwar su ta sanya dole jam'iyyun su sake zaɓe.
Siyasar Najeriya
Samu kari