Tinubu ya Dira Kaduna Don Yakin Neman Zabe, Ya Ziyarci Birnin Gwari Yin Jaje

Tinubu ya Dira Kaduna Don Yakin Neman Zabe, Ya Ziyarci Birnin Gwari Yin Jaje

  • Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, ya ziyarci jihar Kaduna domin gangamin yakin neman zabensa
  • ya samu tarbar Gwamna El-Rufai tun daga filin jirgin sama yayin da ya samu rakiyar Gwamna Ganduje, Atiku Bagudu da Simon Bako Lalong
  • 'Dan takarar shugabancin kasan bai tsaya nan ba, ya garzaya karamar hukumar Birnin Gwari inda ya jajantawa jama'a da harin 'yan bindiga ke ritsawa dasu

Kaduna - 'Dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya dira jihar Kaduna.

Ya je ne domin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna a ranar Talata, Channels TV ta rahoto.

Tinubu a Kaduna
Tinubu ya Dira Kaduna Don Yakin Neman Zabe, Ya Ziyarci Birnin Gwari Yin Jaje. Hoto daga The Governor of Kaduna
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya samu rakiyar abokin tafiyarsa Kashim Shettima da babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

Kara karanta wannan

2023: Jigon dattijon PDP ya caccaki Atiku, ya ce gwamnonin G-5 dole su yi adawa dashi

A cikin tawagarsu akwai da gwamnonin Kano, Abdullahi Ganduje, Kebbi, Atiku Bagudu da Jigawa, Abubakar Badaru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da 'dan takarar gwamna na jam'iyyar APC na jihar, Sanata Uba Sani da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar Kaduna ne suka tarbe su a filin jirgin sama dake Kaduna.

Bayan isowarsa Kaduna, Tinubu ya zarce zuwa karamar hukumar Birnin Gwari, daya daga cikin yankunan da ‘yan bindiga da ‘yan ta'adda suka addaba..

Ya ziyarci yankin ne domin jajanta wa wadanda hare-haren ya ritsa da su da kuma samun kan barnar da hare-haren suka yi.

Tinubu dai ya kwashe tsawon sa’o’i biyu da rabi ne zuwa Birnin Gwari ta kan titi, cikin tsauraran matakan tsaro.

Ya samu rakiyar gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da 'dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani da ‘yan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kano: Mutanen Ganduje Zasu Jagoranci Tawagar Yakin Neman Zaben Gwamna a Jam'iyyar Kwankwaso

Bayan taron Gidan Chatham, Tinubu da tawagarsa sun rakashe

A wani labari na daban, bayan kammala taron Gidan Chatham dake Landan da Tinubu ya halarta, sun girgije tare da rakashewa da tawagarsa a wurin wata liyafar cin abincin dare.

A bidiyon da ya bayyana, an ga 'dan takara kujerar shugabancin kasan yana kwasar rawa bayan sautin da aka sakar masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel