Jam'iyyun Biyu Sun Hada Kai, Sun Ayyana Wanda Zasu Mara Wa Baya Ya Zama Shugaban Kasa

Jam'iyyun Biyu Sun Hada Kai, Sun Ayyana Wanda Zasu Mara Wa Baya Ya Zama Shugaban Kasa

  • Wasu manyan jam'iyyu biyu a Najeriya sun kulla ƙawance, sun ce zasu kawo karshen APC da PDP a zaben 2023
  • Jam'iyyun da suka haɗa da AAC da wani tsagin PRP, sun ayyana Omoyele Sawore a matsayin wanda zai fafata da Atiku, Tinubu
  • Yakin neman zabe ya kara kankama a dukkanin jam'iyyun siyasa a Najeriya, watanni ƙasa da uku ya rage

Abuja - Jam'iyyar The African Action Congress (AAC) da tsagin jam'iyyar PRP sun sanar da cewa sun haɗa kawance da juna gabanin babban zaɓen 2023.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa jam'iyyun sun kuma gabatar da Omoyele Sawore na jam'iyyar AAC a matsayin wanda zasu haɗu su mara wa baya ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Omoyele Sawore.
Jam'iyyun Biyu Sun Hada Kai, Sun Ayyana Wanda Zasu Mara Wa Baya Ya Zama Shugaban Kasa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Sun sanar da curewa wuri guda ne a wurin taron manema labarai da suka kira ranar Litinin 12 ga watan Disamba, 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

Vanguard tace Mista Sawore ne ya wakilci AAC yayin da Abdulmajeed Dauda ya wakilci tsagin jam'iyyar PRP tare da wasu mambobin jam'iyyun biyu a wurin taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar zaɓe INEC ta sanya sunan Falalu Bello a matsayin sahihin shugaban PRP na ƙasa tare da Kola Abiola, ɗa ga Moshood Abiola a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Meyasa suka haɗa wannam ƙawance?

Da yake jawabi kan majar da suka yi, Mista Sawore yace haɗin guiwa tsakanin cikakkiyar AAC da jam'iyyar PRP ta kudiri aniyar kawo karshen mamayar siyasa da APC da PDP suka yi a Najeriya.

Sawore yace:

"Ƙawance ne tsakanin cikakkiyar AAC da PRP, idan kuna son sanin ko har yanzun Kola Abiola na nan cikin tseren ku garzaya ku tambaye shi. Yana ɗaya daga cikin masu nuna kansu a matsayin ɗan takarar PRP."

Kara karanta wannan

Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango

"Ba ruwanmu da bangaren PRP na Kola Abiola, munn haɗa kai ne tsagin PRP da Malam Aminu Kano ya bari."
"Sauran jam'iyyun da kuke gani basu da banbanci, abinda muka sani APC ta ginu ne da waɗanda suka gudu daga jam'iyyar PDP."

Babban Malami Ya Fito Fili, Ya Faɗi Wanda Ba Abinda Zai Hana Shi Zama Shugaban Kasa a 2023

A wani labarin kuma Shahararren Malami a Jihar Legas yace ba abinda zai iya dakatar da Bola Tinubu daga zama shugaban ƙasa a 2023

Fasto Adam Tunji, yace duk da sukar da Bola Tinubu yake kan ɗauko abokin takara Musulmi, ya amince shi ne zai samu nasara a shekara mai zuwa.

Ya shawarci CAN ta maida wukarta kube domin a halin yanzu babu wanda zai iya maida Najeriya ƙasar Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262