APC Ta Shiga Tasku a Arewa, Atiku Ya Tarbi Wadanda Suka Sauya Sheka Daga APC a Nasarawa

APC Ta Shiga Tasku a Arewa, Atiku Ya Tarbi Wadanda Suka Sauya Sheka Daga APC a Nasarawa

  • Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya karbi sabbin wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP
  • An gudanar kamfen takarar shugaban kasa a jihar Nasarawa, Atiku ya bayyana kadan daga alkawuransa
  • Shugaban PDP ya ce yana da kwarin gwiwar PDP za ta ci nasara a zaben mai zuwa na 2023 da ake tunkara

Jihar Nasarawa – Mambobin jam’iyyar APC akalla 10,000 ne a jihar Nasarawa suka bayyana yiwa jam’iyyar saki uku tare da auran jam’iyyar PDP ta adawa, rahoton Punch.

Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ne ya yi musu wankan shiga jam’iyyar PDP a yayin taron gangamin kamfen da aka gudanar a jihar ta Nasarawa.

A cewar Atiku, wadanda tsoffin mambobin APC sun yanke shawara mai kyau, kuma za su ga sakamakon shiga jam’iyyar PDP idan ya yi nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Bayan rantsar dashi, kotu ta kwace kujerar shugaban karamar hukuma a jihar Arewa

Ya kuma yi tsokaci game mulkin ‘yan koyo da APC ke yi a kasar nan, kama daga matakin jiha kar zuwa matakin shugaban kasa.

'Yan APC sun sauya sheka zuwa PDP
APC Ta Shiga Tasku a Arewa, Atiku Ya Tarbi Wadanda Suka Sauya Sheka Daga APC a Nasarawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce akwai karancin samun romon dimokradiyya a mulkin APC, inda yace sam hakan bai dace ba kuma zai tabbatar da an samu sauyi nagari da kowa zai mora.

Atiku ya yiwa matasan Nasarawa alkawarin damawa dasu, tare da samar musu da ayyukan yi a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.

Ya kuma bayyana cewa, zai kawo ayyukan da za su habaka tattalin arzikin Nasarawa kana ya gina titunan da za su hada jihar da makwabtanta.

A cewarsa:

“Idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasan Najeriya a 2023, zan ware $10bn don kirkirar damammakin ayyuka ga matasa da mata a kasarmu.
“Bari na sanar da ku cewa gwamnati na za ta gina tituna da za su hada Nasarawa da jihohin makwabta. Saboda haka, muna son dukkanku ku bamu kuri’unku kamar yadda kuka bamu a zaben da ya gabata.”

Kara karanta wannan

Yadda APC da LP Ke Tsara Dabarun Hana Jam’iyyar NNPP Kai Labari a Jihar Kano

PDP za ta samu kaso 95% na kuri’un ‘yan Nasarawa

A bangare guda, shugaban PDP na kasa ya ce akwai hasashen Atiku ya kawo kuri’un jihar Nasarawa duba da wasu dalilai na siyasa, inda yace tabbas kaso 95% na kuri’un jihar na PDP ne, rahoton Premium Times.

A tun farko da yake jawabin maraba, dan takarar gwamnan PDP a jihar, David Ombugadu ya bayyana kwarin gwiwar cewa, taron zai haifar da mai ido.

A nasa bangaren, dan takarar gwamnan PDP David Ombugadu a jihar ya ce da gani wannan taro na PDP zai haifar da mai ido nan da zaben 2023.

Dana tun farko wan jigon PDP ya bayyana Nasarawa daga jihohin da Atiku zai kawo kaso 95% na kuri'u a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel