2023: A Dawo Min Da Kudin Fom Dina, Dan Takarar Jam'iyyar Su Peter Obi a Kano Ya Fusata
- Osita Nwankwo ya nemi jam'iyyar Labour Party ta dawo masa da kudin da ya siya fom din tsayawa takara a zaben 2023
- Fusataccen dan jam'iyyar na su Peter Obi ya nemi takarar tikitin dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Fagge a jihar Kano amma bai samu ba
- Bayan watanni shida da zaben fidda gwani, Nwankwo ya ce shugabancin jam'iyyarsa ya ki dawo masa da kudinsa N500,000
Kano - Wani fusataccen dan jam’iyyar Labour Party da ya nemi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Fagge ta jihar Kano, Osita Nwankwo, ya nemi a dawo masa da kudin fom dinsa N500,000.
Nwankwo ya bukaci hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, tsawon lokaci bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa bukatar ta Nwankwo ya biyo bayan shugabancin jam’iyyar ya hana masa tikiti domin ya wakilci mazabar Fagge ta Kano a majalisar tarayya.
An tattaro cewa jam’iyyar ta ki ba Nwanko tikitin saboda ya ki biyan miliyan N5 da shugabancin LP ya bukata, rahoton Opera News.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake magana a kan bukatarsa, Nwankwo ya ce:
"Na biya kudin da ake magana a kai a cikin asusun Labour Party mai lamba 1021575052, tare da bankin UBA da 20634382, tare dai da UBA a ranar 6 ga watan Yuli, 400,000 kudin fom da kuma 100,000 na daga kafa kasancewar ni ba dan jam'iyyar bane kafin zaben.
"Na biya 100,000 cikin asusun mai bayar da shawara kan shari'a, duk dai a bankin UBA, gaba daya na biya N500,000 tare da takardar shaida da ke nuna na biya din."
N90,000 kawai aka dawo mun da shi
Nwankwo ya bayyana cewar jam'iyyar ta bukaci ya biya abun da zai iya biya na tikitin sannan bisa ra'ayin kansa ya biya N500,000, wanda jam'iyyar ta ki yarda.
Ya ci gaba da cewa:
"Na rubutawa shugabancin LP wasika a hukumance inda na bukaci a dawo mun da N500,000 na tunda an baiwa Abubakar wanda ya cika sharadinsu tikitin.
"Watanni shida bayan na bukaci hakan daga shugabancin jam'iyyar, babu amsa daga bangarensu, don haka nake amfani da wannan damar don neman a dawo mani da kudina, tunda tabbaci ne cewa jam'iyyar bata da niyan biyana kudina, duk da ta baiwa wani dan takara tikiti da ya biya kudin da aka ce."
Bugu da kari, Nwankwo ya ce jam'iyyar ta dawo masa da N90,000 daga cikin kudin da ya biya na fom din sha'awar tsayawa takara.
2023: Jam'iyyar LP Ta Fara Kulla-Kullar Kawo Karshen Mamayar Ganduje da Kwankwaso a Kano
A wani labarin, jam’iyyar Labour Party ta su Peter Obi ta shirya taro a jihar Kano, domin sanin hanyar da za ta bi ta yi nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban jam'iyyar a jihar Kano, Muhammad Raji ya bayyana cancantar dan takararsu na shugaban kasa tare da tallata shi a gaban jama'a.
Asali: Legit.ng