2023: Saura Kwana 70 Zabe, Shugaban INEC Ya Tona Danyen Aikin da ‘Yan Siyasa Suke Yi

2023: Saura Kwana 70 Zabe, Shugaban INEC Ya Tona Danyen Aikin da ‘Yan Siyasa Suke Yi

  • Kwamishinan INEC, Mallam Mohammed Haruna ya yi jawabi a wajen taron da NESSACTION ta shirya
  • NESSACTION ta fito da shirin #YourVoteMatters da nufin ganin mutane sun karbi katin PVC saboda zaben 2023
  • Kungiyar USAID, IFES da sauran kungiyoyin Duniya suna goyon bayan aikin NESSACTION a Najeriya

Abuja - Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta zargi wasu ‘yan siyasan Najeriya da sayen katin zabe watau PVC daga hannun mutane.

Daily Trust ta rahoto shugaban INEC na rikon kwarya kuma kwamashinanta, Mallam Mohammed Haruna yana cewa ana neman hanyar magudi.

Jami’in hukumar zaben kasar ya ce baya ga sayen katin PVC da bata-garin ‘yan siyasa suke yi, ana biyan kudi domin karbar lambar VIN na mutane.

Mohammed Haruna wanda shi ne Kwamishinan INEC da ke kula da Nasarawa, Kaduna, Filato, Kaduna da FCT ya bayyana wannan ne ranar Litinin.

Kara karanta wannan

A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

An fito da shirin #YourVoteMatters

Kungiyar NESSACTION masu sa-ido a kan harkar zabe sun kaddamar da wani shiri na #YourVoteMatters domin wayar da kan al’umma kan hakkokinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wajen taron ne Mohammed Haruna ya yi jawabi, har ya tona irin badalar da wasu suke yi a kasar da kuma irin kokarin da hukumar INEC take yi a kai.

NYSC INEC
Zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana ram da masu sayen PVC

Kwamishinan hukumar ya ce kwanan nan aka yi nasarar daure wasu mutum biyu a Sokoto da Kano bayan an same su da PVC ta hanyar da ba ta dace ba.

“Mu na da masaniya cewa kusan wasu ‘yan siyasa na sayen katin PVCs. Idan ka karbi PVC, sai ka saida, ko kyale wani dabam ya gani, kana taimakawa wajen mallakar PVC ta haramtaciyyar hanya, wanda laifi ne a dokar zabe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Da sanyin safiyar nan 'yan bindiga suka kone ofishin INEC a wata jiha, uku sun mutu

Wasunku suna da labari cewa kwanan nan, hukumar INEC tayi nasarar daure wasu mutane biyu da aka samu da laifin mallakar PVC ta haramtacciyar hanya a Kano da Sokoto.
Saboda haka ina kira ga mutane su adana PVC dinsu da kyau, su tabbata ranar zabe sun fita da shi wajen kada kuri’a, domin kuwa idan babu PVC, babu yadda za a iya yin zabe.”

- Mallam Mohammed Haruna

NESSACTION ta shiga Abuja da kewaye

Shugaban NESSACTION, Eniola Cole ta bayyana cewa za su fara aiki a jihohin Nasarawa, Filato da Birnin Tarayya wajen ganin mutane sun karbi PVC.

An rahoto Eniola Cole tana mai cewa za su taimakawa hukumar INEC wajen ganin aadadin masu dauke da katin PVC na kada kuri’a sun karu a zaben 2023.

Sanusi II ya ce za a ga sauyi a 2023

A karshen darasin Madarijis Salikeen, an samu rahoto cewa Khalifa Muhammad Sanusi II ya yi tsokaci a kan dokar hana cire fiye da N20, 000 a duk rana.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Tsohon Gwamnan na CBN ya ce babban banki zai yi maganin amfani da kudi da ake yi wajen sayen kuri’un talakawa lokacin zabe saboda su zarce kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel