Siyasar Najeriya
An samu tashin hayaniya a tsakanin tsagin jam'iyyar Labour Party (LP) a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa. Ɓangarorin biyu sun yi musayar kalamai.
Gwmanan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ce yana tare da waɗanda jam'iyyar APC mai mulki ta zaɓa a kason shugabancin majalisar tarayya ta 10 .
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa jam'iyyar APc a jihar, za ta kauce daga kan madafun ikon jihar na wani ɗan lokaci ne kawai.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa zai miƙa mulkin jihar ga zaɓaɓben gwamnan jihar, Rev. Fr. Hyacinth Alia, kafin ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Za a ji Hon. Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu sun samu goyon bayan Gwamnoni da ‘yan jam’iyyun PDP, LP, NNPP da sauran masu adawa a zaben majalisar wakilai.
Uwar jam'iyyar APC ƙasa ta ɗauki mataki, ta soke dakatarwar da aka yi wa sanata Barnabas Gemade, Farfesa Terhemha Shija da wasu mutum biyar a jihar Benue.
Tsaffin ƴan majalisar jam'iyyar APC sun nuna goyon bayan su ga takarar Akpabio da Barau Jibrin, ta zama shugabannin majalisar dattawa ta 10. Sun ce sun cancata.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, hakan ya jawo ana ta surutu.
Tawagar 'yan majalisun jam'iyyun hamayya 6 sun hakura da takarar kujerar kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa, sun ce da yuwuwar su koma bayan na APC.
Siyasar Najeriya
Samu kari