Jam'iyyar APC Ta Nada Manyan Lauyoyi 12 Da Zasu Kare Nasarar Tinubu a Kotu

Jam'iyyar APC Ta Nada Manyan Lauyoyi 12 Da Zasu Kare Nasarar Tinubu a Kotu

  • Jam'iyyar APC ta naɗa lauyoyin masu matsayin SAN guda 12 domin su kare nasarar Bola Tinubu a Kotu
  • INEC ta sanar da ɗan takarar shugaban kasa na APC a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa
  • Sai dai sakamakon bai yi wa manyan jam'iyyu daɗi ba kuma sun lashi takobin kalubalantar sakamakon a Kotu

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta zaƙulo manyan lauyoyi 12 a Najeriya (SAN) domin su kare nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ƙarar da aka shigar kan zaben shugaban kasa.

Tawagar lauyoyin karkashin jagorancin Lateef Fagbemi, ta ƙunshi mashawarci kan harkokin shari'a na APC ta ƙasa, Ahmad Usman El-Marzuq.

Bola Tinubu.
Jam'iyyar APC Ta Nada Manyan Lauyoyi 12 Da Zasu Kare Nasarar Tinubu a Kotu Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Kwamitim kamfen shugaban kasa na jam'iyyar APC ya wallafa jerin sunayen SANs din da jam'iyyar ta naɗa domin kare Tinubu a shafin Tuwita ranar Talata.

Jerin lauyoyi masu darajar SAN da APC ta naɗa

1. Lateef Fagbemi (Shugaban tawaga)

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Sam Ologunorisa, SAN

3. Rotimi Oguneso, SAN

4. Olabisi Soyebo, SAN

5. Gboyega Oyewole, SAN

6. Muritala Abdulrasheed, SAN

7. Aliyu Omeiza Saiki, SAN

8. Tajudeen Oladoja, SAN

9. Pius Akubo, SAN

10. Oluseye Opasanya, SAN

11. Suraju Saida, SAN

12. Kazeem Adeniyi, SAN.

"Muna da kwarin guiwar wannan tawaga na da gogewa da kwarewa da zasu tabbatar da samun nasarar APC a shari'ar da ta shafi korafi kan zaɓen shugaban kasa."
"Muna rokon mambobin jam'iyya su marawa wannan tawaga baya a ƙoƙarinta na kare martabar muradi da zaɓin 'yan Najeriya."
"Haka nan muna kira ga sauran jam'iyyun da ke cikin wannan ƙara da su nuna waye wa da kwarewa wajen biyayya ga tanadin doka daga farko zuwa ƙarshen shari'ar."

- APC ta wallafa a shafinta na Tuwita.

A ranar 1 ga watan Maris, hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ayyana Asiwaju Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Manyan jam'iyyu kamar LP da PDP sun yi watsi da sakamakon, inda suka yi zargin cewa an tafka kura-kurai kuma an take tanadin kundin dokokin zaɓe.

Hukumar INEC Ta Dakatar da Kwamishinan Zabe Na Jihar Sakkwato

A wani labarin kuma Hukumar zaɓe INEC ta dakatar da kwamishinanta na jihar Sakkwato har sai baba ta gani

A wata wasiƙa da ta aike wa reshen hukumar na jihar, ta umarci Sakatariyar gudanarwa ta maye gurbinsa nan take.

Wasu bayanai da muka samu ta bayan fage sun bayyana dalilin da yasa INEC ta dauki mataki kan REC na jihar Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel