Hakan Ba Zai Taimake Ka Ba: Tinubu Ya Caccaki Atiku Kan Yin Zanga-Zanga a Abuja

Hakan Ba Zai Taimake Ka Ba: Tinubu Ya Caccaki Atiku Kan Yin Zanga-Zanga a Abuja

  • Bola Ahmad Tinubu ya caccaki Atiku Abubakar kan yin zanga-zangar kalubalantar sakamakon zabe
  • Tinubu ya ce, zanga-zangar ba za ta tsinana masa komai ba, don haka ya saukakewa kansa aiki ya karbi faduwa
  • PDP da mabiyanta sun yi zanga-zanga a Abuja don nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasa na bana

FCT, Abuja - Zababben shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Vanguard ta ruwaito.

Tinubu ya zargi Atiku kan jagorantar zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu.

Idan baku manta ba, a ranar Litinin, 6 ga watan Maris ne Atiku ya jigoranci dukkan ‘yan a mutun PDP a zanga-zangar da ke adawa da nasarar Tinubu.

Tinubu ya caccaki Atiku kan zanga-zangar kalubalantar zabe
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

An ga ‘yan PDP sanye da bakaken kaya a hedkwatar hukumar zabe ta INEC da ke Abuja, inda suka nemi a soke zaben shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin Tinubu ga Atiku da PDP

Yayin da Tinubu ke martani ga yunkurin su Atiku ta bakin mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga a cikin wata sanarwa, ya ce ya kamata Atiku ya gane cewa, shure-shure bai hana mutuwa.

A cewar Tinubu, Atiku ya riga ya fadi zabe, don haka kawai yana yin abu ne kamar kora kunya da hauka.

A cewar wani yankin sanarwar:

“Ban ga ta inda zanga-zangar da Atiku ya jagoranta za ta taimake shi wajen samun nasara shi da jam'iyyarsa.”

Yadda zaben bana ya kasance

Idan baku manta ba, a zaben bana an ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe, yanayin da ya sa Atiku ya zama sau shida yana neman kujerar shugaban kasa yana rasawa.

Atiku ya tunkari kotu a zaben bana domin kalubalantar zaben tare da cewa, an yi magudin da bai amince dashi ba, BBC Hausa ta tattaro.

Hukumar zabe ta INEC kuwa cewa ta yi, Tinubu ya lashe zaben ne kaso 37% na kuri’un da ‘yan Najeriya suka kada.

Yadda Atiku ya jagoranci zanga-zanga a Abuja

A tun farko kun ji cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jagoranci gangamin zanga-zanga a Abuja.

An ga Atiku da daukacin manyan PDP suna bayyana kokensu ga sakamakon zaben shugaban kasa na bana.

Ya zuwa yanzu, kotu ta ba Atiku da Peter Obi damar duba takardun aikin zaben bana don gano inda aka samo matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel