Majalisa ta 10: APC Zata Miƙawa Kudu Maso Gabas Shugabancin Majalisar Sanatoci

Majalisa ta 10: APC Zata Miƙawa Kudu Maso Gabas Shugabancin Majalisar Sanatoci

  • Ra'ayin jam'iyyar APC yazo ɗaya dake nuna za'a iya miƙawa mutanen yankin Kudu maso Gabas kujerar shugaban majalisar dattawan.
  • Za'a bawa Arewa ta tsakiya da Kudu maso Kudu mataimakin majalisar dattawa da mataimakin majalisar wakilai.
  • Yayinda ake shirin Arewa Maso Yamma ta fitar da shugaban majalisar wakilan tarayya

A yayin da aka kammala zaɓen Sanatoci, kuma ake shirin basu takardar shaidar cin zaɓuɓɓukan ga mambobi.

Yanzu kuma hankula ya koma sama yayin da shaho yaɗauko Giwa. Batu ake akan shugabancin majalisar, na neman wanda ya dace ya jagoranci majalisar dattawan Najeriya

To saidai alamu na soma baiyana ƙarara cewar, jam'iyyar APC mai mulki zata kai Shugabancin majalisar dattawan Najeriya ga ɓangaren Kudu maso gabas ne, saboda sassauta raɗaɗin mutanen yankin da suke ji na rasa Shugabancin ƙasa.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

senate
Majalisa ta 10: APC Zata Miƙawa Kudu Maso Gabas Shugabancin Majalisar Sanatoci
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya daga can ciki tace tunda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yazo ne daga Kudu maso yammacin Najeriya, mataimakin sa daga Arewa maso gabas.

Ra'ayi yazo ɗaya dake nuna, za'a iya miƙawa mutanen yankin Kudu maso Gabas wajen fito da sahihin mutum dazai zama shugaban majalisar dattawan.

Wani jigo a jam'iyyar APC daya buƙaci a ɓoye sunansa ne yace, manyan jam'iyyar na APC ne sukai amanna da cewa kai kujerar can yankin zaisa a samu daidaito na muƙami a ƙasar.

Hakan, kamar yadda jigon ya bayyana, tuni yasa jam'iyyar APC ta soma tuntuɓar sauran yankunan, domin samun sahalewar su akan wannan batu.

A cewar sa:

"Tunda basu samu takarar shugabancin ƙasa ba a dukkan jam'iyyu, a lokacin da inyamurai ke kira abasu ƙasar su, abune mai kyau APC ta basu kujera mafi daraja uku zuwa ga Kudu Maso Gabas," inji shi.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1

Ya kuma ƙara da cewa, Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Kudu ana sa ran zasu samu mataimakin majalisar dattawa da mataimakin majalisar dokoki. Sannan kuma Arewa Maso Yamma zata fitar da shugaban majalisar dokoki.

Majiyar tamu ta Guardian ta ƙara da cewa, shirye shiryen sunyi nisa domin haɗuwa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ƙarƙarewa.

Majiyar ta ƙarkare da cewa:

"Tun 2015, raba shugabanci a APC ba'a adalci. Shi yasa a majalisa ta 10 muke so muyi adalci, tunda yanzu mune muke da mafiya rinjayen yan majalisa da 57 na kujeru.
"A lokacin zaɓen fidda gwani na cikin gida, Kudu maso kudu, basu samu goyon bayan Jam'iyyar na samun ɗan takara ba. Hakan yasa basuji dadi ba. amma yanzu, wata dama ce da zamu nunawa kowa cewa, APC jam'iyyar kowa ce".

Matashi Mara Hannuwa Ya Zama Tela, Yake Ɗinka Kaya

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

Lallai babu nakasashshe sai rago, wani matashi musaki mara hannuwa ya ƙi yarda zuciyar sa ta mutu, inda yaje ya koyi sana'ar ɗinki.

A wani bidiyo da ya yaɗu a TikTok, yana nuna yadda matashin yake sarrafa keken ɗinki cikin ƙwarewa .

Bidiyon ya nuna cewa matashin baya da hannuwa inda suka yi kama da gundulmi alamar kamar an yanke su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel