Kotun Zabe Zata Soma Sauraren Koke-Koken INEC, Tinubu Atiku, da Obi

Kotun Zabe Zata Soma Sauraren Koke-Koken INEC, Tinubu Atiku, da Obi

  • INEC tace idan ɓera ma nada sata, daddawa nada wari. Saboda haka itama tana da ƙorafi.
  • Peter Obi Yana so abashi dama yayi habzi da na'urar BVAS tare da yin ido huɗu da ita.
  • INEC ta farga da dabarar da ƴan siyasan suke na keta mata haddi a matsayin hukuma mai yanci. Yau dai za'a soma jin ƙorafe korafen.

Zaɓuka sun kammala, korafe korafe suna ci gaba da fantsama a cikin ƙasa tun bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya da kuma na Sanatoci.

A ƙoƙarin da take wajen ganin ta warware wadannan korafe korafen, an kafa wata kotu ta musamman don sauraron korafe-korafe.

Zaben
Kotu ta Musamman Don Sauraren Korafe Korafen Zaɓe Zata Soma Sauraren Koke-Koken INEC, Tinubu APC, Obi da LP Asali: UGC
Asali: Facebook

Kotun ta musamman ana sa ran zata soma zama ne a yau da yamma, kuma daga cikin manya manyan ƙorafe korafen da ake fatan kotun zata saurara akwai wanda INEC na neman a dakatar da izinin da kotu ta bawa PDPn Atiku Abubakar da LP ɗin Perter Obi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Izinin kuwa da aka basu shine na basu damar zuwa suyi binciken ƙwaƙwaf akan kayayyakin zaɓen da INEC ta tattara yayin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun daya gabata.

Duk a yau din dai, kotun tana fatan sauraran ƙorafin da aka shigar na zaɓen da akayi wa Bola Ahmed Tinubu na ranar 6 ga watan Maris, domin neman sahalewa aje a duba kayan zaɓen da akai amfani dasu a ranar.

Bayanin da The Nation online ta nuna, ta sanar da cewa ɗaya daga cikin ƙararrakin da za'a saurara sun hada dana Obin Labor Party, dake fatan a bashi dama yaje yayi binciken bin ƙwaƙwƙwafi tare da duba BVAS a zahiri.

Karin bayanai na nan tafe....

Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Nemi Mambobinta Da Su Zaɓi Ƴan Taƙarar Jam'iyyar Kaɗai

Ana dab da a fara zaɓen gwamna, jam'iyyar Labour Party, ta fito tayi wani muhimmin kira ga mambobin ta.

Jam'iyyar ta nemi mambobin ta da magoya bayan ta da su tabbatar ƴan takarar jam'iyyar kawai suka zaɓa a zaɓen ranar Asabar Jam'iyyar ta kuma musanta jita-jitar cewa tayi haɗaka da wasu jam'iyyun a zaɓen da za a fafata na ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel