Ko da Gwamnonin G5 Sun Hada Ba, Ba Za Su Kawo Atiku Ba, Inji Sanata Shehu Sani

Ko da Gwamnonin G5 Sun Hada Ba, Ba Za Su Kawo Atiku Ba, Inji Sanata Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, gwamnonin G5 masu adawa da Atiku ba za su iya taimaka masa ya ci zabe ba ko da sun hada kai
  • Sani ya ce, yana da matukar muhimmanci a gane cewa, gwamnonin ba za su iya taimakawa tafiyarsu ta siyasa ba balle taimakon wani
  • Ya kuma shaida cewa, matasan Najeriya sun kwace kujeru da yawa daga tsoffin ‘yan siyasa, kuma alamu sun nuna abin ya fara fin karfinsu

Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya sake sakin magana mai zafi kan gwamnonin G5 na jam’iyyar PDP masu adawa da Atiku Abubakar.

Sani, a cikin wani rubutun da ya yada a Twitter ya ce, gwamnonin ba za su iya taimakon kansu ba balle kuma daura dan takarar shugaban kasa ya gaji Buhari.

Kara karanta wannan

"Sun Gaza Taimakon Kansu": Shehu Sani Ya Zolayi Gwamnonin G5 Bayan Shan Kayen Atiku

Gwamnonin na G5 dai sun hada da Nyesom Wike na jihar Rivers, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da Samuel Ortom na jihar Benue.

Shehu Sani ya yi magana kan gwamnonin G5
Sanata Shehu Sani kenan na jihar Kaduna | Hoto: Olubiyo Samuel
Asali: UGC

A yayin da ake kan ganiyar gangamin shugaban kasa gabanin zaben 25 ga watan Faburairu, gwamnonin sun ce basu amince da shugabancin PDP ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar gwamnonin G5 a baya ga Atiku

Gwamnonin G5, ta bakin gwamna Wike sun yi kira ga dan takarar shugaban kasa na PDP kan ya tabbatar da tsige shugaban jam’iyyar na kasa, Ayu Iyorchia.

Wannan yasa bore ya tashi a PDP, har ta kai dan takarar shugaban kasa, Atiku ya fadi a zabe ba tare da taimakon ko daya daga cikin gwamnonin na G5 ba.

Sai dai, da yake bayani, Shehu Sani ya ce dama gwamnonin ba za su iya tsinanawa kansu komai ba balle su iya taimakawa dan takarar na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ainihin Dalilan da Suka Jawo APC Ta Ji Kunya a Legas, Kaduna, Katsina da Jihohi 9

Ba za ku tsinana komai ba

A cewarsa:

“Ko da ace gwamnonin G5 sun marawa mai girma Atiku baya, babu tasirin da hakan zai yi. Sun gaza taimakawa kansu balle kuma dan takarar shugaban kasansu.
“Sun gaza gane talakawa sun waye da bin makahon umarni daga gwamnoni; gwamnoni yanzu roko suke.”

A halin da ake ciki, an yi zaben shugaban kasa a Najeriya, kuma Atiku Abubakar na PDP ya fadi, amma ya ce ba zai hakura ba, ya tafi kotu har ma batu ya kai ga zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel