Siyasar Najeriya
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya nuna jin dadinsa kan yadda fadar shugaban kasa ta ki tanka wa kan kalaman da Peter Obi ke yi.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan gayyatar da Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Gwamna Abba ta shiga jam'iyyar APC.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki daya daga cikin abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar bayan ya bukaci da ya yi murabus idan ba zai iya ba.
Ministan harkokin ci gaban ma'adanai, Dele Alake ya nesanta kansa da dukkan fastocin yakin neman zaben da ke yawo a soshiyal midiya cewa zai nemi takara a Ekiti.
Kotun Kolin Najeriya ta yi fatali da karar tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar HDP wanda ya nemi soke nasarar Buhari a 2019 da nasarar Tinubu a 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya fito ya yi magana kan batun neman shugabancin jam'iyyar APC na kasa da aka yada cewa yana da muradi.
Mambobin majalisar dokokin jihar Ogun sun kaɗa kuri'at ba gudu ba ja da baya a matakin tsige kakakin majalisar, sun rantsar da wanda zai maye gurbinsa yau Talata.
Jam'iyyar APC mai mulki ta gargaɗi tsohon gwamnan jihqr Kogi, Yahaya Bello, ya shiga taitayinsa doomin babu gurbinsa a kwamitin gudanarwa na ƙasa karkashin Ganduje.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya koka kan yadɗa rikicin siyasar jihar Ribas ya zame masa karfen kafa, ya hana shi zama cikin farin ciki da iyalansa.
Siyasar Najeriya
Samu kari