Rigima Ta Kaure Tsakanin Magoya Bayan APC da PDP Kan Abu 1, Shugaban Jam'iyya Ya Raunata

Rigima Ta Kaure Tsakanin Magoya Bayan APC da PDP Kan Abu 1, Shugaban Jam'iyya Ya Raunata

  • An shiga tashin hankali a ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa bayan rigima ta kaure tsakanin magoya bayan PDP da APC kan kayan zaɓe
  • Rahoto ya nuna yamutsin ya tashi ne yayin da jami'an INEC suka fara kokarin sauke kayan zaɓe a kauyen Twon Brass jetty
  • Shugaban PDP na ƙaramar hukumar ya samu rauni sanadin rigimar wanda sojoji suka kai ɗauki aka shawo kan lamarin

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - An shiga yanayin tashin hankali a garin Twon Brass jetty da ke ƙaramar hukumar Brass a jihar Bayelsa kan kayayyakin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC).

Rigima ta ɓalle tsakanin APC da PDP a Bayelsa.
Bayelsa: Tashin Hankali Yayin da Magoya Bayan APC da PDP Suka Yi Arangama Kan Kayan Zabe Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Hatsaniya ta ɓarke a garin yayin da jami'an hukumar zaɓe INEC mai zaman kanta suka fara kokarin sauke kayayyakin zabe ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo: Akwai yiwuwar ba za a yi zabe ba bayan an samu sabani kan muhimmin abu 1

Lamarin ya auku ne bayan saɓani ya shiga tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da PDP kan wurin da ya kamata a sauke kayayyakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Brass mai suna, Bara Daniel ya samu rauni a wannan rigima da ta faru yayin sauke kayan zaɓe.

Duk da magoya bayan APC karkashin jagorancin Victor Isaiah, tsohon shugaban karamar hukumar ne ake zargi da tada yamutsin, Isaiah ya musanta cewa yana da hannu a ɓarnar da aka yi.

Ya ce maimakon haka shi ya kawo ɗauki saboda rashin da’a da ake zargin Mista Daniel ya yi na tsoratar da magoya bayan APC kan yadda za a sauke kayan zaben.

“Na je ne domin sa ido a kan yadda za a sauke kayan amma shugaban PDP ya yi ta kalamai na batanci wanda hakan ya tunzura wasu a wurin kuma ni na yi kokarin yayyafa wa lamarin ruwan sanyi."

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Wane matakin jami'an tsaro suka ɗauka?

A halin yanzu, bayanai sun nuna cewa dakarun sojoji sun kai ɗauki wurin kuma komai ya koma daidai, zaman lafiya ya dawo.

Sai dai Shugaban karamar hukumar Brass, Mista Alabo Hanson Karika, ya yi kakkausar suka ga harin da aka kai wa shugaban PDP na karamar hukumar.

Karika ya yi kira ga jami'an tsaro da su kasance a ankare domin daƙile faruwar hakan nan gaba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Atiku ya je jihar Kogi

A wani rahoton kuma Atiku Abubakar da tawagarsa sun dira jihar Kogi domin taya Dino Melaye kamfen takarar gwamna a zaben ranar Asabar.

A wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa mai kunshe da Hotuna, an ga manyan jiga-jigan tare da juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262