Sanatar PDP Ta Gaza Riƙe Kanta a Zauren Majalisar Dattawa, Ta Zubda Hawaye Kan Rasuwar Babban Sarki
- Sanata Natasha Akpoti ta gaza riƙe jimamin da ta shiga, ta zubda hawaye a majalisar dattawan Najeriya kan rasuwar Sarkin Ebiraland
- Ta zubda hawaye ne yayin da take gabatar da kudiri kan rasuwar Basaraken a zauren majalisar ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba
- Majalisar dattawan ta yi shirun minti ɗaya daga bisani kuma ta aminta da bukatar da ke ƙunshe a cikin kudirin
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawa ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama marigayi Sarkin ƙasar Ebira watau Ohinoyi na Ebiraland, Abdulrahman Ado Ibrahim.
Bayan haka Majalisar ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta karrama marigayi Sarkin ta hanyar canza sunan kwalejin ilimi da tarayya da ke Okene zuwa sunansa.
Majalisar dattawan ta kuma yanke shawarar turawa da wasikar ta'aziyya domin jajantawa iyalai da mutanen masarautar Ebiraland kan wannan rashi, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatocin sun cimma wannan matsaya ne biyo bayan nazari da kuma aminta da kudiri mai taken, "Rasuwar Ohinoyi na ƙasar Ebira, Dokta Abdulralman Ado Ibrahim."
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa ce ta ɗauki nauyin gabatar da kudirin a zaman ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.
Natasa ta zubda hawaye a zauren majalisa
Sanata Natasha ta gaza riƙe halin jimamin rashin Sarkin da ta shiga, sai dai aka ga ta sa hannu tana share hawayen da ke kwararo wa daga idanunta yayin gabatar da kudirin.
Ta ce majalisar dattijai ta kaɗu da jin rasuwar Ohinoyi na Ebiraland, Dokta Abdulrahman Ado Ibrahim, ranar Lahadi, 29 ga Oktoba, 2023 a asibitin Abuja yana da shekaru 94.
Da suke bada tasu gudummuwar, Sanatoci sun jinjina wa marigayi Sarkin tare da amincewa da buƙatar da ke ƙunshe a kudirin da aka gabatar musu.
A karshe, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya nemi kaɗa kuri'ar murya kan kudirin wanda kuma gaba ɗaya Sanatocin suka amince, Tribune ta rahoto.
Ni ake son kashe wa - Ajaka
A wani rahoton kuma Murtala Ajaka ya zargi Gwamna Yahaya Bello da amfani da wasu jami'an tsaro domin cimma burinsa na raba shi da duniya.
Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar SDP ya ce manufar harin da aka kai Dekina shi ne a kashe shi amma ya tsallake.
Asali: Legit.ng