Siyasar Najeriya
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya dora alhakin rikicin jihar Rivers a kan Gwamna Siminalayi Fubara. Wike ya ce gwamnan ba ya bin umarnin kotu.
Babbat kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta yi hukunci kan shari'ar da jam'iyyar Labour Party ta shigar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Tsohon mataimakin shugaba APC na Arewa maso Y?amma, Salihu Lukman ya ce kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 zai zama abin wahala ga 'yan siyasar adawa.
Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin hadakar Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi inda ta ce babu wani abin tsoro a gare ta saboda dukansu yan son rai ne.
Karamar jam'iyya ta APP ta lashe zabe a kananan hukumomin Rivers yayin da PDP da APC suka fadi. Rikicin Fubara da Wike na cikin abubuwan da suka jawo nasarar APP.
Ana zargin cewa wasu bata gari sun cinnawa sakatariyar karamar hukumar Eleme wuta awanni bayan rantsar da sababbin ciyamomin kananan hukumomin Ribas.
Jam'iyyar LP ta nuna amincewa da Rabi'u Musa Kwankwaso ya zamo mataimakin Peter Obi a zaben 2027. LP ta ce Peter Obi ya samu kuri'u sama da Kwankwaso a 2023
Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin yin wani gagarumin sauyi a majalisar ministocin kasar nan inda zai bayyana jerin sunayen ministocin da sababbin ministoci.
Fitaccen dan gwagwarmaya a yankin Neja Delta, Asari Dokubo ya gargadi rundunar sojoji da yan sanda a jihar Rivers bayan ganin jirgi na shawagi a saman gidansa.
Siyasar Najeriya
Samu kari