Atiku Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Sa Aka Gaza Gyara Najeriya

Atiku Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Sa Aka Gaza Gyara Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya magantu kan shekara guda da shugaba Bola Tinubu ya shafe a karaga
  • Atiku Abubakar ya bayyana irin hanyoyi marasa ɓullewa da shugaba Bola Tinubu ya bi wajen kawo Najeriya halin da take ciki a yau
  • Ya kuma bayyana abubuwan da suka zama dole shugaban kasa ya aiwatar idan yana son kawo canji mai ma'ana ga 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta azabtar da yan Najeriya cikin shekara daya.

Atiku da Tinubu
Atiku Abubakar ya ce Tinubu ya gaza cikin shekara guda. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya soki shekarar farkon Tinubu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Atiku Abubakar na cewa mulkin Tinubu ya zama kamar bulaliyar kan hanya wacce bata bar talaka da mai kudi ba.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun siyasa sun yi kewar Buhari, ana Allah wadai da shekarar farko a mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya kuma kara da cewa tsare-tsare masu tsauri da Bola Tinubu ya kawo sun kori masu zuba jari da dama daga ƙasashen ketare.

Mulkin Tinubu ya ruguza kasuwanci

Alhaji Atiku Abubakar ya ce tsare-tsaren da Tinubu ya bullo da su musamman a harkokin tattalin arziki sun nakasa yan kasuwa a kasar.

A cewarsa, hakan ya sa talakawan na kara shiga kangin talauci masu kuɗi kuma na talaucewa a faɗin kasar, rahoton Leadership.

Tsadar rayuwa a mulkin Tinubu

Atiku Abubakar ya kara da cewa an samu tashin farashin kayyakki mafi muni a tarihin Najeriya a mulkin Bola Tinubu.

Ya ce a watan Afrilu an samu tashin kayan abinci da kashi 40.53% wanda shi ne mafi muni a shekaru 15 da suka wuce.

Mulkin Tinubu: Ayyuka da aka rasa

Atiku Abubakar ya ce kamfanoni irinsu Unilever, Bolt Food, Equinor da sauransu duk sun fice daga Najeriya saboda tsauraran matakan da gwamnatin ta dauka.

Kara karanta wannan

"Kano ta kama hanyar kamawa da wuta," Jigo ya buƙaci Tinubu ya dakatar da Gwamna Abba

'Dan siyasar ya ce hukumar NECA ta bayyana cewa sama da kamfanoni 15 suka fice daga Najeriya wanda yasa an rasa ayyuka kimanin 20,000.

A karshe Atiku Abubakar ya ce matuƙar ana son fitar da Najeriya daga halin da take ciki dole sai Bola Tinubu ya saka tausayi cikin mulki wajen rage tsauraran matakan da ya dauka.

Jam'iyyun adawa za su yi hadaka

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya yi karin haske kan maganar hadakarsa da Atiku Abubakar

Peter Obi ya ce matuƙar aka samu daidaito kan yadda za a magance matsalolin Najeriya a tsakaninsu zai goyi bayan haɗakar dari bisa dari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng