Za Ka Ji a Jikinka": An Bayyana Jerin Kalaman Jonathan Ga Buhari Kafin Barin Mulki

Za Ka Ji a Jikinka": An Bayyana Jerin Kalaman Jonathan Ga Buhari Kafin Barin Mulki

  • An gano abin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fadawa Muhammadu Buhari lokacin da zai bar mulki
  • Jonathan ya fada cewa gwmnatin da za ta gaje shi za ta fuskanci matsaloli da dama marar misaltuwa
  • Bayan saukar Jonathan, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya gaji kujarar a shekarar 2015 har zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gargadi Muhammadu Buhari lokacin barin kujerar mulki.

Jonathan ya ce yana tausayin gwamnatin da za ta karbi mulki a wancan lokaci inda ya nuna damuwa kan halin da za su tsinci ƙasar.

Yadda Jonathan ya gargadi Buhari kafin barin mulki
Muhammadu Buhari ya gaji shugabancin Najeriya daga Goodluck Jonathan a 2015. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Gargadin Jonathan ga Buhari a 2015

Kara karanta wannan

Kano: Jawabin karshe da Sanusi II ya yi kafin maida shi gadon sarautar Dabo

Tsohon hadimin Jonathan, Doyin Okupe shi ya tabbatar da haka a cikin wani faifan bidiyon YouTube yayin hira da Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okupe ya ce mai gidansa ya yi hasashen halin da kasar za ta shiga tun a wancan lokaci yayin da zai bar mulki.

Tsohon hadimi ya ce Jonathan ya fada masa cewa gwamnatin da za ta karbi mulki za ta fuskanci matsaloli.

"Lokacin da zamu bar mulki, ana saura kwanaki kadan mu bar ofishin mulki ina tare da Goodluck Jonathan a cikin wani yanayi."
"Na tambaye shi Oga lafiya kuwa? Sai ya ce yana tausayawa gwamnatin da za ta gaje shi."
"Ya ce za ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa da kalubale."

- Doyin Okupe

Buhari ya gaji mulki daga Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya gaji kujerar Jonathan bayan kayar da shi a zaben 2015.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Daga bisani, Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 inda ya sake yin nasara kafin kammala wa'adinsa a shekarar 2023.

Bayan kammala wa'adinsa ne a shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya karbi ragamar mulkin kasa zuwa yanzu.

Buhari ya taya Tinubu murna

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murnan cika shekara daya a kan mulki.

Buhari ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su ci gaba da ba Tinubu goyon baya domin inganta rayuwar ƴan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.