Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ƴar Takarar Gwamna da Wasu Shugabannin Jam'iyya 4

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ƴar Takarar Gwamna da Wasu Shugabannin Jam'iyya 4

  • Yayin da ake tunkarar zaben gwamna, APC ta dakatar da ƴar takarar da ta nemi tikitin gwamna a zaɓen fidda gwanin Ondo, Folake Omogoroye
  • Jam'iyya mai mulki ta kuma dakatar da wasu shugabannin APC a gundumar Ode Aye da ke ƙaramar hukumar Okitipupa a jihar Ondo
  • A sanarwar da jam'iyyar ta fitar, ta ce ta dakatar da ƴar takarar ne bisa zargin cin amana da yi wa APC zagon ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - All Progressives Congress (APC) ta gundumar Ode-Aye a karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo ta dakatar da Injiniya Folake Omogoroye.

Injiniya Folake Omogoroye ita ce ƴar takara mace da ta fafata a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar ranar 20 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

APC v SDP: Kotun zabe ta yanke hukunci kan shari'ar takarar gwamnan jihar Kogi

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar APC ta dakatar da ƴan takarar gwamna mace a jihar Ondo Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Ta zama ‘yar takarar gwamna ta baya-bayan nan da APC ta dakatar bayan irin wannan matakin ladabtarwa da aka dauka kan Sanatan Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC Ondo ta dakatar da shugabanni 4

Jam'iyyar APC ta dakatar da ƴar takarar tare da wasu shugabannin jam'iyya huɗu na gundumar Ode Aye I, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.

Waɗanda aka dakatar tare da Omogoroye sun haɗa da sakataren tsare-tsaren jam'iyya, Ayesan Tunde da mataimakin kakakin jam'iyya, Jemiken Seyi.

Sauran su ne mataimakin sakataren walwala, Adebayo Omobayo da kuma mataimakin ma'ajiyin APC duk a gundumar, Eweje Omotayo.

Dakatar da Omogoroye na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na gundumar, Akinsowola Awodele. 

Meyasa jam'iyyar APC ta dakatar da su?

A cewar wasikar, an dakatar da Omogoroye ne saboda, "zargin cin amanar jam'iyya da kuma rashin biyayya ga shugabannin da aka naɗa."

Kara karanta wannan

Kotu ta watsawa APC kasa a ido, ta tabbatar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa

Idan ba ku manta ba ƴar takarar gwamnan na cikin waɗanda suka yi fatali da sakamakon zaben fitar da gwani wanda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya samu nasara.

Ta kuma yi kira da a soke zaɓen gaba ɗaya saboda an tafka kura-kurai kuma ta shigar da ƙara kotu inda ta ƙalubalanci nasarar Gwamna Aiyedatiwa, Vanguard ta rahoto.

APC na shirin kwace Kudu maso Gabas

A wani rahoton kuma mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar APC, Paul Chukwuma ya yi magana kan muradunsa na takara.

Paul Chukwuma ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin APC mai mulkin Najeriya idan ya zama gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel