Manyan Abubuwa 3 da Suka Faru a Siyasar Najeriya Daga 1999 Zuwa 2024

Manyan Abubuwa 3 da Suka Faru a Siyasar Najeriya Daga 1999 Zuwa 2024

  • Kungiyoyin fararen hula sun yi gwagwarmaya da shugabannin mulkin soja kafin a dawo mulkin dimokuraɗiyyar a Najeriya
  • Bayan dawowa mulki dimokuraɗiyya a shekarar 1999, abubuwan da suka shafi siyasar Najeriya da dama sun faru
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa uku da suka fin jan hankalin al'umma tun dawowar dimokuraɗiyyar Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyoyin fararen hula sun yi gwagwarmaya da a lokutan mulkin soja kafin a dawo mulkin farar hula a shekarar 1999.

Najeriya
Zanga zangar karin kudin mai a 2012 na cikin manyan lamuran da suka faru a Najeriya. Hoto: Femi Johnson
Asali: Facebook

Daga shekarar 1999 zuwa yau abubuwan ban al'ajabi da badakala kala-kala sun faru a siyasar Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Legit ta tatttaro maku guda uku (3) daga cikin manyan abubuwan da suka faru a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shugaban majalisa da takardar bogi

Tun farkon kafa dimokuraɗiyya a shekarar 1999 aka samu shugaban majalisar wakilai ya yi amfani da takardun bogi domin tsayawa takara.

Dan majalisar wakilai da ya fito daga Kano, Ibrahim Salisu Buhari ya yi amfani da takardar digiri da bautar ƙasa na bogi kafin a gano shi daga baya.

2. Tazarcen shugaban kasa Obasanjo

Bayan kammala shugaban kasa karo na biyu, Olusegun Obasanjo ya fara kokarin hawa mulki karo na uku.

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kokarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasa domin ba Obasanjo damar takara karo na uku amma hakan bai samu ba.

3. Zanga-zangar cire tallafin mai

A shekarar 2012 shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara kudin mai daga N65 zuwa N141 a kan duk litar man fetur.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Hakan ya sa al'ummar Najeriya yin zanga-zanga tare da yajin aiki a fadin Najeriya. Zanga-zangar ta tilastawa gwamantin Jonathan rage kudin mai zuwa N97.

Tinubu zai binciki gwamnatin Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta bayyana cewa za ta binciki yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayar da jinginar filayen jiragen sama.

A shekarar 2023 gwamnatin tarayya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma na Malam Aminu Kano da ke Kano domin farfado da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel