Ministan Tinubu Ya Koka Kan Yadda Ake Gudunsa Bayan Taimakon Wasu a Zaben 2023

Ministan Tinubu Ya Koka Kan Yadda Ake Gudunsa Bayan Taimakon Wasu a Zaben 2023

  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya yi martani kan yadda ƴan siyasa ke cin amanar iyayen gidansu wadanda suka taimake su a rayuwa
  • Umahi ya bayyana cewa akwai wadanda ya taimake su a zaben da aka gudanar a 2023 suka hau madafun iko amma yanzu suna gudunsa
  • Ministan ya bayyana haka ne a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi a yau Alhamis 30 ga watan Mayun da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi ya koka kan yadda ake cin amana a siyasa.

Umahi ya ce mafi yawan wadanda ya taimake su suka samu mulki a zaben 2023 yanzu gudunsa suke yi.

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun sutu a harin 'bam' da aka kai masallacin Kano

Ministan Tinubu ya magantu kan cin amanarsa da aka yi a siyasa
Ministan ayyuka, Dave Umahi ya koka kan yadda ake cin amana a siyasa. Hoto: @realdaveumahi.
Asali: Twitter

Umahi ya ce yaransa suna gudunsa

Ministan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umahi ya ce hatta 'yan Majalisar Tarayya da ya taimakawa suna gudunsa yanzu sai dai ya ce ko a jikinsa bai damu ba, Punch ta tattaro.

"Cif Onyekachi Nwebonyi ne kadai zai iya kira na mai gidansa, amma sauran suna tsoron gwamna zai yi fushi da su."
"Gwamnan ba zai yi haka ba saboda shi ma kansa yana fada da ni ne sanadin nasararsa a cin zabe."

- Dave Umahi

Babu lokacin yaki da Nwifuru - Umahi

Umahi ya ce zai yaki da duk wanda ke neman fada da gwamnan jihar saboda ya cancanci mutuntawa daga gare su gaba daya.

Ministan ya ce kamar yadda ake samun matsala tsakanin gwamna da mai gidansa shi ba shi da wannan lokaci a yanzu inda ya ce zai ba shi dukkan goyon baya.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin Kano ya yi magana bayan an tashi da sarakuna 2 a gari

Kotu ta hana gwamna binciken Ortom

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun jiha da ke Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth binciken tsohon gwamna, Samuel Ortom.

Kotun ta ce akwai korafi da Ortom ya shigar wanda ke buƙatar daukar mataki kafin ba da bahasi kan binciken.

Wannan na zuwa ne bayan Hyacinth ya kaddamar da kwamitin bincike guda biyu a watan Faburairu kan tsohon gwamnan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel