Siyasar Najeriya
INEC ta ce ADA, ATP, AAP da wasu kungiyoyi 11 ne kacal suka tsallake tantancewar farko ta zama jam'iyyar siyasa a cikin kungiyoyi 171 da suka nema.
Wata Kungiyar siyasa a jihar Kano da ta kunshi malaman Musulunci sun yi karatun Alkur'ani mai girma saboda samun nasara a zaben 2027 ga Bola Tinubu da Barau Jibrin.
Wata kungiya a jihar Ondo da ke samun goyon baya daga ministan harkokin cikin gida ta kudiri aniyar shiga gida gida domin tallata tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da ake shirye-shirye zaben 2027, wasu majiyoyi suka ce Goodluck Jonathan da magoya bayansa na kokarin jawo Rabiu Kwankwaso domin tafiya tare.
A labarin nan, za a ji yadda NNPP ta bayyana illar da ta hango, wanda ya tilasta mata korar wasu daga cikin ƴan majalisa da su ka ci zaɓe a inuwar jam'iyyar.
APC reshen jihar Bayelsa ta amince wa Shugaba Tinubu ya yi tazarce a 2027, amma rashin Lokpobiri da Lyon ya sake jawo tambayoyi kan rikicin cikin gida na jam’iyyar.
Bayan tsawon watanni ana dako da rigingimu, hukumarzabe ta kasa, INEC ta amince da sababbin shugabannin jam'iyyar ADC karkashin Sanata David Marka.
Yayin da ake shirye-shiryen zaben shekarar 2027, Fasto Josiah Onuoha ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben duk da rikicin da ke cikin APC.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gaji da yadda wasu 'yan siyasa a Najeriya su ka fara amfani da dabaru wajen fara kamfen.
Siyasar Najeriya
Samu kari