Siyasar Najeriya
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta bayyana cewa yawan sauya shekar da jiga-jigan 'yan adawa suke yi zuwa APC, ba zai hana jam'iyyar faduwa ba a zaben 2027.
Adelabu ya ce hadin kai ne zai dawo da APC mulki a Oyo, ya yi alkawarin kammala tashoshin wuta uku, gyaran hanyoyi da hadin kai da TAMPAN da OAPs.
APC ce mai rinjaye a Majalisar Dattawa, bayan wasu ‘yan majalisa sun sauya sheka daga PDP da sauran jam’iyyu. Daga kujeru 59 a 2023, yanzu APC na da sanatoci 75.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dakatar da shugabanta a jihar Edo. Jam'iyyar ta bayyana cewa an dakatar da shi bayan an same shi da wasu laifuffuka.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gamsu da irin goyon da jam'iyyar APC ke samu. Ya bayyana cewa za ta samu kuri'u masu yawa a zaben shekarar 2027.
Wasu lauyoyi suna ganin cewa ficewar Gwamna Douye Diri daga PDP ya sabawa doka, yayin da wasu ke cewa hakan na iya sa ya rasa mukaminsa Na gwamna.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ya zargi APC da rashin kwarin gwiwa da danniya ga ‘yan adawa, yana mai cewa ADC za ta karbi mulki daga Tinubu a 2027.
Rauf Aregbesola ya zargi APC da jawo yunwa, talauci da rashin tsaro a Najeriya, yana mai cewa ADC ce zabin jama'a wadda za ta cika alkawuranta a 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa babu adawa anjihar wadda ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Siyasar Najeriya
Samu kari