Siyasar Arewa
Gwamnatin Bola Tinubu ta amince da samar da motoci masu aiki da wutar lantarki 10,000 a wasu Arewa maso Gabas. Za a samar da wuraren cajin motocin.
An fara yakin neman zaben shugaba Bola Tinubu domin tazarce a jihohin Arewa. Jiga jigan APC sun fara kamfen a jihohin Arewa da suka hada da Kaduna da Kebbi.
Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin sun sake raba PDP da ɗaruruwa magoya bayanta a Arewa.
Yayin da gwamna Bala Mohammed zai kammala mulkinsa a 2027, Sanata Ahmed Abdul Ningi ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027 karkashin PDP.
Ministan lafiya, Ali Pate ya ce yana da burin yin takarar gwamnan Bauchi a 2027, amma yanzu ya mayar da hankali kan aikin da Shugaba Tinubu ya ba shi.
Wasu da ake zargin masu goyon bayan Sanata Babangida Hussaini a Jigawa sun yi wa tsohon hadimin Badaru Abubakar duka kan sukar mai gidansu a gidan rediyo.
Kungiyar SOKAPU ta sake daura damara don samun jihar Gurara, tana tattaunawa da mahukunta, tana mai cewa jihar za ta iya dogara da kanta idan an ƙirƙire ta.
Kungiyar Arewa Consultative Forum ta bayyana cewa matukar gwamnati ba za ta dauki matakin da ya dace a kan kisan direbobin Arewa ba, za a fuskanci barazanar tsaro.
Majalisar Shira ta tsige shugaban karamar hukumar, Abdullahi Beli, da mataimakinsa bisa zarge-zargen rashawa. An nada Hon. Wali Adamu a matsayin mukaddashi.
Siyasar Arewa
Samu kari