Kisan Direbobi: Dattawan Arewa Sun Yi Kaca Kaca da Gwamnati da Jami’an Tsaro
- Dattawan Arewa sun bayyana takaicinsu kan yadda wasu 'yan ta'adda a Kudu maso Gabashin Najeriya ke kashe direbobinta
- Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan IPOB da ESN sun kashe akalla direbobin Arewa 20 da ke safarar kaya zuwa yankinsu
- Amma, a cewar ACF, gwamnatin tarayya da jami'an tsaro ba su dauki matakan da suka dace na dakile kisan da zai iya zama barazana ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Kungiyar ACF ta bayyana damuwarta kan hare-haren da ake kai wa direbobin manyan motocin da ke safarar kaya daga Arewa zuwa Kudu maso Gabas.
Ana zargin cewa ‘yan kungiyar awaren Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke neman balle wa daga Najeriya ne ke kai hare-haren.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ACF ta yi gargadi cewa kisan direbobin da kuma kona motocinsu babbar barazana ce ga tsaron kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta Arewa ta kara da nusar da gwamnati cewa wadannan kashe-kashen na iya haddasa rugujewar doka da oda tare da jefa kasa cikin fitina da rudani.
ACF ta yi tir da kisan ‘yan Arewa
Jaridar Blueprint ta wallafa cewa Sakataren yada labaran ACF na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya ce kungiyar ba ta jin dadin hare-haren da ake kai wa direbobin manyan motocin Arewa ba tare da wani dalili ba.

Asali: Facebook
ACF ta zargi hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya da gazawa wajen dakile wadannan hare-hare, yayin da kashe-kashen direbobi, kona motocinsu da satar kayayyaki ke ci gaba da faruwa.
Kungiyar ta ACF ta ce:
“Wadanda ke ikirarin kasancewa ‘yan kungiyar ta’addanci irin su IPOB da Eastern Security Network (ESN), suna kai hare-haren ne kawai kan ‘yan Arewa da kadarorin Arewa.”
“Wadannan ‘yan ta’adda suna kara kaimi wajen kai hare-haren ta’addanci, har ma suna wallafa bidiyoyin sakamakon munanan ayyukansu a shafukan sada zumunta suna alfahari da abinda suka aikata. A lokuta da dama, cin zarafin yana kai ga kona gawarwakin wadanda aka kashe.”
Direbobi sun yi zanga-zangar kisan 'yan Arewa
A ‘yan kwanakin nan ne 'yan kungiyar masu motocin dakon kaya ta kasa (NARTO) da kungiyar direbobin manyan motoci ta kasa (NURTW) sun gudanar da zanga-zanga a Jos, Jihar Filato.
An gudanar da zanga-zangar ne da nufin jawo hankalin jama’a kan hare-haren da suka janyo mutuwar direbobi fiye da 50 da kona akalla tireloli 100 a cikin shekaru takwas da suka gabata.
DSS ta gayyaci ‘yan jarida kan kisan ‘yan Arewa
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gayyaci ‘yan jaridar Daily Trust a Jihar Filato a ranar Talata, sakamakon rahoton da suka wallafa kan zanga-zangar da aka yi kan kisan direbobin Arewa.
Jaridar ta ruwaito cewa direbobi da masu motocin dakon kaya sun gudanar da zanga-zanga a Jos a ranar Lahadi, inda suka bayyana damuwarsu kan yadda ake kashe membobinsu.
Rahoton ya ce akalla direbobi 20 ne aka kashe, yayin da da dama suka bace a hare-haren da aka kai musu a Kudu maso Gabas cikin shekara guda da ta gabata.
ACF ta yi takaicin karuwar rashin tsaro
A baya, kun ji cewa kungiyar ACF ta bayyana takaicinta kan yadda ake kara fuskantar matsalar rashin tsaro a jihohin Arewa, tare da nuna fargabar cewa lamarin na iya kamari.
Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu, da ya bayyana wannan fargaba, ya ce idan aka zura ido, rashin tsaro na iya shafar yawancin jihohin da ke yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng