Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa a Bauchi

Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa a Bauchi

  • Majalisar kansilolin Shira ta tsige shugaban karamar hukumar, Hon. Abdullahi Ibrahim Beli, da mataimakinsa Hon. Usman Adamu
  • Daga cikin kansiloli 18, 16 sun amince da tsige Hon. Abdullahi da Usman bayan kwamitin bincike ya tabbatar da zarge zargen da ake yi masu
  • An nada Hon. Wali Adamu a matsayin mukaddashin shugaban karamar hukumar Shira har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Majalisar kansilolin karamar hukumar Shira, a jihar Bauchi, ta tsige shugaban karamar hukumar, Hon. Abdullahi Ibrahim Beli, da mataimakinsa, Hon. Usman Adamu.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsige su ne saboda zarge-zargen rashin da’a, almundahana, gazawa wajen gudanar da ayyukansu, da kuma cin zarafin ofis.

Majalisar /shira ta bayyana dalilin tsige shugaban karamar hukumar da mataimakinsa
Bauchi: Kansiloli sun taru sun tsige shugaban karamar hukumar Shira. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Majalisar ta ayyana kujerun shugaban da mataimakinsa a matsayin wadanda babu kowa kansu har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsige ciyaman da mataimakinsa a Bauchi

A cikin wata wasika da ta aika wa majalisar dokokin jihar Bauchi a ranar Litinin, an bayyana cewa tsige shugabannin zai fara aiki daga ranar 3 ga Maris, 2025.

Hon. Wali Adamu, shugaban majalisar kansiloli, da Hon. Abdullahi Wada, mataimakinsa, ne suka rattaba hannu kan wasikar tsige shugabannin.

A cewar wasikar, an kafa kwamitin bincike wanda ya tabbatar da cewa ciyaman da mataimakinsa sun aikata abubuwan da ake zarginsu da su.

Daga cikin kansiloli 18 da ke karamar hukumar Shira, 16 sun amince da matakin tsige shugabannin bayan duba rahoton kwamitin.

Bauchi: Majalisa ta zabi mukaddashin ciyaman

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Hon. Wali Adamu ya ce an dauki wannan mataki ne bayan bin ka’idojin doka.

Ya bayyana cewa an sha jan hankalin shugaban karamar hukumar kan matsalolin amma ya ki gyarawa, sannan ya kasa kiran taron majalisa kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Akpabio da shugabanni da jami’ai 3 da aka taba tuhuma da cin zarafin mata

Bayan nazarin rahoton kwamitin bincike, kansilolin sun amince gaba daya da matakin tsige shugaban karamar hukumar da mataimakinsa don ci gaban yankin.

Majalisar karamar hukumar ta ayyana Hon. Wali Adamu, shugaban majalisar kansiloli, a matsayin mukaddashin shugaban karamar hukumar Shira.

An nada shi a matsayin mukaddashin shugaban har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe don cike gurbin ciyaman da mataimakinsa.

Jerin kansilolin da suka goyi bayan tsige ciyaman

Kansiloli duba rahoton kwamitin bincike, sun tsige shugaban karamar hukumar Shira.
Jerin kansilolin da suka rattaba hannu a takarardar tsige shugaban karamar hukumar Shira. Hoto: Labari daga Bauchi
Asali: Facebook

Daga cikin kansilolin da suka amince da matakin akwai Hon. Umar Garba (Bangire), Hon. Garba A. Haladu (Bukul), da Hon. Babangida Umar (Disina A).

Sauran sun hada da Hon. Garba Sadi (Disina B), Hon. Usman Bello (Dango), Hon. Ishaqa A. Mamuda (Faggu B), da Hon. Dalhatu A. Haruna (Gagibida).

Har ila yau, akwai Hon. Al Hassan Mohammed (Kilbori A), Hon. Garba Bello (Kilbori B), Hon. Ayuba Buhari (Shira), da Hajiya Hadiza Adamu (Beli).

Kara karanta wannan

Natasha: Atiku ya tsoma baki a zargin shugaban majalisa da neman lalata

Sauran kansilolin da suka goyi bayan matakin sun hada da Hon. Aminu Umar (Tsafi) da kuma Hon. Magaji Mohammed (Zubo).

An tsige ciyaman da ke rigima da gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, takaddamar siyasa tsakanin Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, da shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙara tsamari.

Majalisar kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, Dakta Kelly Ehidiamen Inedegbor da na karamar hukumar Akoko-Ado, Tajudeen Alade.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.