Siyasar Arewa
Nasir El-Rufai, ya lissafa wasu muhimman abubuwa 4 da ba zai taba mantawa da su a lokacin da mulkinsa na shekaru 8 a Kaduna ba. Daya daga ciki shi ne korar malamai.
Yan takara 200 da suka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Kaduna tare da magoya bayansu akalla 10000 sun tattara kayansu daga NNPP, sun koma SDP.
’Yan kasuwa a Kaduna sun goyi bayan Uba Sani, Shugaba Boa Tinubu da APC, yayin da suka yi ikirarin cewa sun sha wahalhalu a lokacin mulkin Mallam Nasir El-Rufa’i.
An samu sabon tsagin shugabanci a jam'iyyar SDP reshen Kogi. An ce hakan ya haddasa rikici inda tsagin Moses Oricha ya yi watsi da sabon shugaban da 'yan kwamitinsa.
Mallam Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Kaduna da tsare Jafaru Sani bisa laifin da ba na hurumin jihar ba. Tsohon gwamnan ya yi Allah ya isa kan kama Jafaru.
Rikicin shugabanci ya kunno kai a cikin jam'iyyar SDP a jihar Kogi bayan sauya shekar Nasir El-Rufa'i. Shugaban jam'iyyar ya bukaci taimakon INEC da SSS.
Alhaji Attahiru Bafarawa ya musanta shiga SDP, yana mai cewa labaran ba su da tushe. Ya shaida cewa yanzu ya mayar da hankali kan gina rayuwarsa a wajen siyasa.
Gwamnatin jihar Gombe ta karyata zargin shugaban SDP na jihar Gombe da ya ce gwamna Inuwa Yahaya ya nemi ya zabga masa mari a filin jirgin sama da suka hadu.
Wata ƙungiyar matasa a Arewacin Najeriya mai suna 'Young Nigerian Voices' ta bukaci tsohon minista, Hon. Emeka Nwajiuba ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Siyasar Arewa
Samu kari