Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
A wani faifai da aka fito da shi, an ji Abdullahi Ganduje bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya zauna da Rabiu Kwankwaso ba, Gwamnan ya na magana kamar ya yi kuka.
Sarkin Kano ya ba Bola Tinubu shawarar yadda za a kawo karshen rigimar addini, ya bayyana haka ne da yake magana da yawun Hakimin Nasarawa, Babba Dan-Agundi.
Gaskiya sun fito kan tayin da Bola Tinubu ya yi wa Rabiu Kwankwaso. Sannan zababben shugaban Kasar ya zauna da Mai martaba Muhammadu Sanusi II a kasar Faransa.
Muhammadu Sanusi II ya ce dole gwamnati ta daina biyan kudin tallafin fetur, ya na da ra’ayin za a tsiyace muddin ba ta cire hannunta a kan lamarin mai ba.
Sarkin Ife yana so a ajiye bangarancin siyasa, a mara baya ga gwamnati mai zuwa, ya ce kyau a hadu tare a goyi bayan manufar Asiwaju Gbogbo Oodua (Bola Tinubu).
Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Joe Igbokwe, ya caccaki tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, kan kalaman da ya yi akan Yemi Osinbajo.
Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya ce ƙasar nan ta tafka babbar asara rashin samun mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a matsayin shugaban ƙasa.
Yaron tsohon Sarkin Kano, ya ce babu wani laifi da mahaifinsu ya aikata, illa sukar Gwamnati, ya ce tofa albarkacin baki kan tattalin arziki bai saba doka ba
Za a ji a ranar Asabar ne Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yi fita cikin kayan sarauta yayin da mutane su ke ta surutu a kan yiwuwar komawarsa mulki.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Samu kari