Yanzu Yanzu: Abba Gida-Gida Ya Gayyaci Sanusi Zuwa Bikin Rantsar Da Shi

Yanzu Yanzu: Abba Gida-Gida Ya Gayyaci Sanusi Zuwa Bikin Rantsar Da Shi

  • Gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci tsohon sarki Muhammadu Sabusi II zuwa bikin rantsar da shi
  • Abba Gida-Gida ya ce zuwan Sanusi wajen taron zai kara kawatar da shi kuma hakan zai zama tamkar goyawa tafiyarsu baya ne
  • A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben gwamnan a matsayin mutum na daya a jihar Kano

Kano - Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya gayyaci tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zuwa wajen bikin rantsar da shi, Daily Trust ta rahoto.

A cikin wasikar gayyatar wanda Abba ya sanyawa hannu mai kwanan wata 26 ga watan Mayu, zababben gwamnan ya ce zuwan Sanusi zai kara kawatar da taron kuma zai zama gagarumin gudunmawa a garesu.

Kara karanta wannan

May 29: Muhimman Abubuwa 5 da Mutane Zasu Gani Ranar Bikin Rantsar da Tinubu a Abuja

Muhammad Sanusi II da Abba Kabir Yusuf
Yanzu Yanzu: Abba Gida-Gida Ya Gayyaci Sanusi Zuwa Bikin Rantsar Da Shi Hoto: The Daily Reality
Asali: UGC

Ya ce:

"Kamar yadda ka sani cewa an gudanar da zaben gwamna na 2023 a jihar Kano a ranar 18 ga watan Maris, wanda Allah SWT da ikonsa yasa na zama a matsayin wanda ya lashe zaben sannan hukumar INEC ta bani takardar cin zabe. Saboda haka ina mai farin cikin gayyatarka zuwa bikin rantsar da ni tare da mataimakina, Kwamrad Amin Abdussalam Gwarzo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na yarda cewa zuwanka bikin ba wai kawai zai kara kawata wannan muhimmin taro bane , illa zai kuma zama gagarumin ci gaba da goyon baya a garemu yayin da muka shiga wannan tafiya da nufin dawo da abubuwan da muka rasa da martabar jiharmu mai albarka, ta hanyar mayar da ita kan tafarkin ci gaba da bunkasata a dukkan bangarori. In shaa Allah."

Ba abun mamaki bane idan an gayyaci Sanusi bikin rantsar da Abba Gida-Gida, Kwamitin mika mulki

Kara karanta wannan

Tinubu: Kashim Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

Wani babban mamba a kwamitin mika mulki wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da cikakken bayani game da ci gaban, ya ce kwamitin ya yanke shawarar gayyatan daukacin 'ya'yan jihar domin su halarci wannan taro."

Ya ce duba ga wannan da kuma umurnin kotu da ya soke hukuncin hana Sanusi shiga jihar Kano, ba zai yi mamaki ba idan aka gayyaci tsohon sarkin.

Babu tabbacin Sanusi zai amsa gayyatar ko ba zai amsa ba

Wani hadimin tsohonn sarkin wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatarwa Daily Trust cewa Sanusi ya samu wasikar gayyatan amma bai yanke shawara kan ko zai halarci taron ba.

Ya ce hakan ya kasance ne saboda Sanusi ya samu gayyata biyu na bikin rantsar da shugaban kasa da kuma na rantsar da zababben gwamnan jihar Abia wanda yake tsohon ma'aikacin banki kamar shi.

Sai dai kuma ya tabbatar da cewar shugaban darikar Tijjaniyan ya bar Najeriya zuwa Afrika ta kudu a daren ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Halarci Taron Zababɓen Gwamnan APC, Ya Yi Magana Mai Jan Hankali, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Kano ta wanke Doguwa daga zargin kisan kai

A wani labarin, mun ji cewa ma'akatar shari'a ta jihar Kano ta wanke shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai.

Gwamnatin Kano ta ce ba a sami hujja da ke tabbatar da Doguwa ya aikata laifukan da ake tuhumarsa a kai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel