Sanusi II Ya Ankarar da Tinubu Tun Yanzu, Ya Sake Bada Shawarar Janye Tallafin Fetur

Sanusi II Ya Ankarar da Tinubu Tun Yanzu, Ya Sake Bada Shawarar Janye Tallafin Fetur

  • Muhammadu Sanusi II ya haskawa gwamnatin Najeriya irin hadarin daukar nauyin tallafin man fetur
  • A wani taro da ya halarta, Sarkin Kano na 14 ya ce an yi watsi da muhimman abubuwa a kan saukin mai
  • Sanusi II ya na da ra’ayin gwamnati za ta tsiyace muddin ba ta cire hannunta a kan lamarin man fetur ba

Abuja - Fitattun masana sun tattauna a kan abubuwan da suka shafi tsare-tsaren tattalin arziki, a wannan karo an sake dauko batun cire tallafin man fetur.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya halarci bikin kaddamar da wani littafi da aka yi a Abuja, The Nation ta ce ya bada shawarar a janye tallafin man fetur.

Sarkin Kano na 14 yake cewa tsarin yana da illa ga tattalin arzikin Najeriya, ya ce akwai bukatar gwamnati ta daina biyan kudin domin zai tsiyata kasar.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 20 Ya Sauka, Fashola Ya Nemawa Mutum 383,431 Aiki a Kujerar Minista

Sanusi II
Khalifa Muhammadu Sanusi II Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsohon Gwamnan babban bankin kasar ya na so Bola Tinubu ya tsaida biyan tallafin fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ilmi, asibiti ko fetur mai araha?

Malam Muhammadu Sanusi II ya nanata matsayar da yake kai tun 2011, ya ce talaka ya fi bukatar ilmi, kiwon lafiya da wutar lantarki a kan man fetur da araha.

An rahoto Muhammadu Sanusi II yana cewa a maimakon a rika kashe Dalolin kudi saboda a hana fetur yin tsada, ana watsi da ilmi da abubuwan more rayuwa.

"Abin da ku masu goyon bayan tallafin man fetur ku ke cewa shi ne arahar man fetur ya fi ilmi, kiwon lafiya, lantarki da sauransu a wajen talakan kasar nan.

Idan aka yi wannan na tsawon shekaru 30 ko 40, wace irin kasa za mu samu? Shi ne abin da muke yi."

Kara karanta wannan

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

- Muhammadu Sanusi II

A rahoton da jaridar Leadership ta fitar, Khalifa Sanusi ya nuna tsarin da ake amfani da shi a Najeriya ba tallafin fetur ba ne, ya ce akwai hauka a lamarin.

Dole Gwamnati mai zuwa ta gyara

"Farashin kudin kasar waje zai iya tashi daga N150 zuwa N500 kuma duk gwamnatin tarayya za ta dauki nauyin tallafin man fetur.
Wannan sakarci ne. Ana kama hanyar tsiyacewa ne. Idanunmu a bude, amma mu na dosar tsiya a gabanmu.

- Muhammadu Sanusi II

Mai martaban ya ce idan Gwamnatin da za ta karbi mulki a karshen Mayu ta ce za ta biyewa wannan tsari nan da shekaru uku, zai ce ba da gaske ta ke yi ba.

Siyasar NNPP da APC a Kano

A rahotonmu, Lauyan Abba Kabir Yusuf, Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci ya yi karin haske a kan shari’ar NNPP da APC a kan zaben Gwamnan Kano.

Lauyan 'dan takaran NNPP ya yi kaca-kaca da masu hango Nasiru Gawuna a kujerar Gwamna, ya ce tun farko Jam’iyyar APC tayi kuskure wajen kai kararta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel